'Yan sanda sun damke babban limamin IPOB da layu tare da harsasai

'Yan sanda sun damke babban limamin IPOB da layu tare da harsasai

  • Rundunar 'yan sandan jihar Imo ta yi caraf da wani mutum mai suna Ikechukeu Umaefulem a jihar
  • Ana zarginsa da zama babban limamin kungiyar rajin kafa kasar Biafra a kudancin Najeriya, IPOB
  • An kama mutumin da bindiga, harsasai, abubuwa masu fashewa, tutar Biafra da sauransu a wani wurin bautar gargajiya

Imo - Rundunar 'yan sanda ta sanar da damke babban limamin masu rajin kafa kasar Biafra, IPOB a jihar Imo, Daily Trust ta ruwaito hakan.

Kamar yadda mai magana da yawun rundunar 'yan sanda na jihar, CSP Mike Abattam ya sanar, wanda ake zargi mai suna Ikechukeu Umaefulem, an kama shi ne a wani wurin bautar gargajiya dake karamar hukumar Ikeduru ta jihar Imo.

'Yan sanda sun damke babban limamin IPOB da layu tare da harsasai
'Yan sanda sun damke babban limamin IPOB da layu tare da harsasai. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

Da wadanne miyagun kaya aka kama shi?

Mai magana da yawun rundunar 'yan sandan yace an samu bindiga daya da carbi biyar na harsasai tare da abubuwa masu fashewa, tutar Biafra da sauran kayan tsibbu.

Kara karanta wannan

Sokoto da sauran jihohin Najeriya guda 5, da yadda sunayensu suka samo asali

Ya ce an kama shi ne bayan samamen da ake kaiwa sansanonin IPOB/ESN kuma an samu nasarar halaka wasu tare da tarwatsa kungiyar ta'addanci a jihar.

'Yan kungiyar IPOB/ESN sun saka dokar zaman gida na dole a kowacce ranar Litinin har sai an sako shugabansu, Nnamdi Kanu.

Duk da dai jami'an tsaro suna ta kokarin hana tabbatuwar wannan dokar, miyagun suna ta tada tarzoma tare da tada kayar baya ta hanyar kaiwa jama'a farmaki.

Jami'an tsaro sun sha alwashin sanya kafar wando daya da dukkan masu tada tarzomar tare da tada kayar baya a yankin kudancin.

'Yan ta'addan IPOB sun kone fasinja kan karya dokar zaman gida a Imo

Mambobin IPOB sun kone wani fasinja mai suna Nkwogu a karamar hukumar Ahiazu Mbaise dake jihar Imo sakamakon karya dokar zaman gida na dole da suka saka a ranar Litinin.

Tuni dai dukkannin harkokin kasuwanci suka tsaya a yawancin sassan jihohin kudu yayin da mazauna yankin suke bin dokar da aka saka, Daily Trust ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Jami'an kwastam sun cafke miyagun kwayoyin da aka shigowa da 'yan bindiga

An rufe makarantu yayin da aka hana dalibai masu rubuta jarabawar NECO fitowa domin rubuta jarabawarsu. Daily Trust ta tattaro cewa mamacin yana cikin daya daga cikin motoci bas uku da miyagun suka tsare a titi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng