Sarkin Musulmi ya bayyana abin da ya jawo abubuwa suka tabarbare a kasar nan

Sarkin Musulmi ya bayyana abin da ya jawo abubuwa suka tabarbare a kasar nan

  • Sarkin Musulmi, Muhammad Sa’ad Abubakar ya yi magana game da matsalolin da ake fama da su.
  • Sultan yana ganin cewa akwai sakacin iyaye wajen yadda abubuwa suka jagwalgwale a kasar nan.
  • Sa’ad Abubakar III ya yi wannan bayani ne da ya halarci wani bikin kaddamar da littafi a garin Abuja.

FCT, Abuja - Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar III, yace rashin kular iyaye yana cikin dalilan da yasa ake samun matsaloli a al’umma.

Daily Trust ta rahoto Sarkin Musulmi yana wannan jawabi ne a ranar 9 ga watan Nuwamba, 2021.

Mai alfarma Sultan yana ganin akwai sakacin iyaye wajen kulawa da yaransu da kuma rashin samun kyakkyawar dangataka wajen tabarbarewar al’amura.

Muhammad Sa’ad Abubakar III ya yi wannan bayani ne a birnin Abuja a ranar Litinin a wajen bikin kaddamar da wani littafi da Dr. Yakubu Gambo ya rubuta.

Kara karanta wannan

Kwamitin da yake bincike a kan rikicin EndSARS yace dole a kawo Abba Kyari gabansa

Yakubu Gambo ya rubuta littafi mai suna ‘Evolution of Day Secondary School in Nigeria’ wanda ya yi bayani a kan kaimin makarantun je ka-ka dawo a Najeriya.

Sarkin Musulmi
Sarkin Musulman Najeriya Hoto: @labaridagabauchi
Asali: Facebook

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Abin da Sarkin Musulmi ya fada a taron.

Jaridar tace Mai martaba Sarkin Wase, Dr. Mohammed Sambo Haruna ya wakilci Sultan wajen taron, inda ya nemi iyaye su maida hankali wajen bada tarbiyya.

“A madadin shugabanninmu, ina kira ga dukkaninmu (iyaye), mu koma muyi abin da ya dace. Akwai bukatar mu ba ‘ya ‘yanmu kulawar da suke bukata.”
“Wadansu daga cikin matsalolin da muke fuskanta a yau, suna aukuwa ne saboda (iyaye) ba mu da alaka da ‘ya ‘yan na mu.” – Sarki Mohammed Sambo.

Olusegun Obasanjo ya turo wakili wajen taron

Tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo ya turo shugaban jami’ar NOUN, Farfesa Olufemi Peters, domin ya wakilce sa a wajen wannan taro da aka yi.

Kara karanta wannan

Tsohon Sarkin Kano Sanusi yace sabon littafinsa da zai fito a 2022 zai gigita ‘Yan siyasa

Olusegun Obasanjo ya yi bayanin muhimmancin karatun sakandare, yace shi ne tsani tsakanin firamare da karatun manyan makarantun gaba da sakandare.

Meyasa ba a shiri tsakanin Gumi da Buhari?

Alhaji Tukur Mamu ya bayyana alakar shugaban kasa da Sheikh Ahmad Abubakar Mahmud Gumi, da abin da ya sa Buhari ya rike shehin malamin a rai.

A wata hira da aka yi da shi, mai magana da yawun Dr. Ahmad Gumi yace mutane suna yi wa shehin wata mummunar fassara a kan da batun 'yan bindiga.

Asali: Legit.ng

Online view pixel