Hotunan wasu 'yan Najeriya 4 wadanda suka dawo da miliyan N152.4 da aka tura asusun bankunansu bisa kuskure

Hotunan wasu 'yan Najeriya 4 wadanda suka dawo da miliyan N152.4 da aka tura asusun bankunansu bisa kuskure

Duk da irin kalubalen da 'yan Najeriya ke fuskanta a kullum, akwai mutane da yawa da har yanzu ba za su iya daukar abin da ba nasu ba don wadatar da kansu.

Duk da cewar gaskiya na da alfanu matuka, yin hakan sai mutum ya zamo jajirtacce kuma mai kau da kai daga ci da gumin wasu.

A cikin wannan rahoton, Legit.ng za ta duba wasu ‘yan Najeriya hudu wadanda suka ba mutane mamaki bayan sun dawo da kudaden da aka tura zuwa asusunsu bisa kuskure.

Hotunan wasu 'yan Najeriya 4 wadanda suka dawo da miliyan N152.4 da aka tura asusun bankunansu bisa kuskure
Dukkaninsu sun kamanta gaskiya Hoto: Julius Eze, Sola Ismail, Sunny Anderson Osiebe, Nchetaka Chukujama
Asali: Facebook

1. Julius Eze

A ranar Litinin, 12 ga watan Yuli, Julius ya tafi kai tsaye zuwa banki sannan ya mayar da N2.5m da ya yi kuskuren shiga asusunsa.

Matashin dan Najeriyan ya bayyana cewa kafin ya tunkari bankin domin fara aiwatar da hakan, ya yi bincike don sanin mai kudin.

2. Sola Ismail

Lamarin Sola abu ne mai ban sha'awa. Ta yi odar wani kaya daga wani kamfanin China kan kudi N41,000 kuma ba da daɗewa ba ta gano ba su da shi.

Kara karanta wannan

Tsohuwar Minista ta ce maza su hakura kawai, a mika wa mata ragamar Najeriya

Da ta nemi a dawo mata da kudinta, kamfanin ya ce N38,000 kawai zai mayar mata. Bayan ta yarda ta amince, sai suka yi kuskuren tura mata N38m. Matar ta mayar da kuɗin da ya hau.

3. Josephine Nchetaka Chukujama

Eze Wata mata a jihar Enugu ta mayar da zunzurutun kudi N13,946,400 da aka tura mata a asusun ta yayin da take wani shagon gyaran gashi.

Mijinta, Chukujama, ya yabawa matar tasa kan aikin gaskiya saboda ya ce da wasu mutane ne da sun kashe kudin.

4. Sunny Anderson Osiebe

Sunny ya bada labarin yadda wani kamfani da ke Abuja ya turawa asusunsa da zunzurutun kudi har N98m. Mutumin yace ikon Allah ne yasa shi maida kudin.

Riƙon alƙawari: Tsawon shekaru 30 Bahaushe na kula da dukiyar Bayarabe, ya damƙata ga magada

A gefe guda, wani labari da ya rusa bangon ƙabilanci ya bayyana kuma hakan ya bayar da burin samun makoma mai kyau a gaba.

Kara karanta wannan

Bayan Kame Sunday Igboho, Yarbawa sun magantu kan ra'ayin ballewa daga Najeriya

Wani saurayi dan Najeriya mai dauke da shafin Twitter @sarnchos a ranar Talata, 25 ga watan Mayu, ya bayyana yadda wani bahaushe mai kirki ya kasance mai aminci ga danginsa kusan shekaru 30.

A cikin wallafar farko da ya yi a cikin 2019, ya rubutu yadda mutumin da ya haura shekaru 90 a lokacin yake ta kula da dukiyar mahaifinsa tun bayan rasuwar mahaifin nasa a 1992.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng