Zamfara, Jihohin Arewa ne kan gaba yayin da ‘Yan bindiga suka bindige mutum 1, 031 a kwana 30

Zamfara, Jihohin Arewa ne kan gaba yayin da ‘Yan bindiga suka bindige mutum 1, 031 a kwana 30

  • Sama da mutane 400 aka kashe a Jihohin Zamfara, Kebbi, da Neja a watan Yuni
  • Binciken Beacon Consulting ya nuna watan da ya gabata, an kashe mutum 1, 000
  • ‘Yan ta’adda da masu tada kafar baya irinsu ESN su na hallaka mutane a Najeriya

A yayin da aka hallaka mutane sama da 1, 000 a watan Yunin da ya gabata, jaridar Daily Trust ta ce jihohin Zamfara, Kebbi, da Neja ne su ka ciri bakaken tutoci.

Duk bayan sa'a 24, sai an kashe mutane 34 a Yunin 2021

A cikin wata guda, ‘yan bindiga sun kashe akalla mutum 1, 031. Daga cikin wannan adadi, 275 sun fito ne daga Zamfara, inda ake ta fama da matsalar kashe-kashe.

An rasa mutane 93 da 91 a Kebbi da kuma jihar Neja a cikin kwanaki 30 na watan Yunin 2021.

KU KARANTA: Mutanen da su ka shafe kwanaki 40 a hannun 'yan bindiga, sun fito

Kara karanta wannan

Jami’an tsaro sun ceto mutane 100 da aka yi garkuwa da su a Zamfara a ranar idi

Rahoton ya bayyana cewa wani kamfani mai suna Beacon Consulting ya yi bincike, ya gano cewa an yi awon-gaba da mutane 390 a jihohi 34 cikin watan da ya wuce.

‘Yan bindiga da sauran miyagu sun kai hare-hare akalla 205 da nufin su dauke Bayin Allah, domin a biya kudin fansa kamar yadda binciken da aka gudanar ya nuna.

Beacon Consulting ya yi wa rahotonsu take da “Nigeria Security Report”, inda aka fito da ta’adin da ‘yan fashi, masu garkuwa da mutane da wasu bata-gari su ka yi.

‘Yan bindiga sun shiga kananan hukumomi 127 da ke jihohi 34 a Najeriya. Barnar da aka fi yi shi ne na satar dabbobi da awon gaba da Bayin Allah a cikin kauyuka.

KU KARANTA: 'Yan sanda sun ceto wasu 'Yan makaranta da aka sace a Kaduna

Muhammadu Buhari
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari Hoto: punchng.com
Asali: UGC

Boko Haram sun hallaka mutane tara, sun sace 20. A daidai wannan lokaci, ‘yan bindiga da sojojin ESN na kungiyar IPOB sun kashe kusan mutane 20 a hare-hare 12.

Kara karanta wannan

An yi luguden wuta tsakanin 'yan fasa-kwaurin shinkafar waje da jami'an kwastam

Alkaluman kowane yanki

Jaridar ta ce a yankin Arewa maso yamma ne aka fi kai hare-hare, inda aka rasa mutane 416, aka dauke 289. A Arewa ta tsakiya, mutane 218 suka mutu, an sace 24.

A Arewa maso gabas an kashe mutane 188, daga nan sai Kudu maso gabas, inda aka hallaka mutane 117. Mutane 18 kadai aka kashe a bangaren Kudu maso kudu.

Bayan Zamfara, Kebbi da Neja, a jihar Kaduna ma an kashe mutane 26, kuma an dauke mutane 157. Mutane 72 da 27 aka rasa a Benuwai da Filato a watan na Yuni.

Kun ji cewa tsohon Sarki Muhammadu Sanusi II ya yi idi a Kaduna, ya yi limanci a filin Murtala Muhammad da ke Kaduna, ya gabatar da huduba a kan zaman lafiya.

Gwamna Nasir El-Rufai, Uba Sani da dinbin Musulmai sun yi sallah a bayan Muhammadu Sanusi II

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: Shugaban 'yan fashi ya kai hari kauyukan Zamfara, ya sace mutum 150 saboda an kama mahaifinsa

Asali: Legit.ng

Online view pixel