2023: Rashin tabbas a PDP kan zaben dan takarar shugaban kasa na gaba

2023: Rashin tabbas a PDP kan zaben dan takarar shugaban kasa na gaba

  • 'Yan siyasa a kasar sun yi martani game da kiraye-kirayen da 'yan kudu suke yi na neman yankin ya samar da Shugaban kasa na gaba
  • Wasu mambobin jam'iyyar Peoples Democratic Party sun bayyana cewa yayi wuri da jam’iyyar zata mika tikitinta na Shugaban kasa ga wani yanki a yanzu
  • Kwamitin aiki na PDP na kasa bai cimma matsaya ba game da dan takarar shugaban kasar jam’iyyar na gaba

Wani rahoto da ke fitowa ya nuna cewa Jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) ba ta yanke kowani shawara ba kan yankin da za ta mikawa tikitin takarar shugaban kasa na 2023 ba.

A cewar jaridar The Punch, majiyoyi da yawa daga PDP sun ce ya yi wuri da jam’iyyar za ta yanke hukunci a kan yankin da zai samar da dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar na gaba.

KU KARANTA KUMA: Waiwaye: Bidiyon Shagari yana kunna sigari lokacin da Firayim Minista Tafawa Balewa ke jawabi ga taron jama'a

Kara karanta wannan

Ka Yafe Wa Igbobo, Ya Wahala, Ya Gane Kurensa: Basaraken Yarbawa Ya Roƙi Buhari

2023: Rashin tabbas a PDP kan zaben dan takarar shugaban kasa na gaba
Kwamitin PDP bai yanke shawara kan yankin da zai mika wa tikitin takarar shugaban kasa na 2023 ba Hoto: Prince Uche Secondus
Asali: Facebook

Jaridar, ta bayyana cewa wasu mambobin jam'iyyar da suka yi magana ba tare da bayyana sunansu ba sun nuna bacin ransu game da batun mika mukamin shugaban kasa zuwa kowane yanki na kasar.

An tattaro cewa sun yi jayayya cewa ba daidai ba ne ga jam'iyyar adawa ta rarraba tikitin nata, ba tare da yin la’akari da dabarun da za su sa ta ci zaben 2023 ba.

KU KARANTA KUMA: Matasan Sakkwato sun mamaye fadar Sarkin Musulmi akan kalaman batanci ga Annabi

Tattaunawa game da batun mulkin karba-karba ta sake kunno kai bayan gwamnonin jihohin kudu, a ranar Litinin, 5 ga watan Yuli, sun amince da cewa magajin shugaba Buhari ya fito daga yankin.

Gwamna Yahaya Bello ya soki batun mulkin kara-karba

Sai dai kuma, Gwamna Yahaya Bello na jihar Kogi ya nuna bacin ransa game da matsayin gwamnonin kudu kan batun mulkin karba-karba.

Kara karanta wannan

Limamin coci ya koka kan wahalar da ‘yan Najeriya suke sha a karkashin mulkin Buhari

A cewar jaridar The Cable, Bello ya bayyana cewa mulkin karba-karba ba dole bane tunda ba a amince da shi ba a cikin kundin tsarin mulkin kasar.

Gwamnan ya ce a shekarar 2023, wanda ya fi dacewa shine wanda zai hada kan kasar.

A wani labarin, biyo bayan sauya sheka da wasu gwamnonin jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) da wasu jiga-jigan jam'iyyar suka yi zuwa jam'iyyar All Progressives Congress (APC) mai mulki, fadar shugaban kasa ta ce babbar jam'iyyar adawa ta kasar na iya zama fanko kafin 2023 babban zabe.

Legit.ng ta rahoto cewa mai ba shugaban kasa shawara na musamman kan harkokin yada labarai, Femi Adesina ya bayyana haka a ranar Alhamis, 8 ga watan Yuli, a wani wallafa mai taken, ‘Magana da PDP a harshen da ta fahimta.’

Adesina ya ce ana yi wa PDP magana da yaren da ta fahimta, inda ya kara da cewa tana kururuwar kisan gilla.

Kara karanta wannan

Abdulsalami ya ja kunnen ‘yan siyasa da cewa sauya sheka ka iya haddasa husuma

Asali: Legit.ng

Online view pixel