Fadar Shugaban kasa ta yi hasashen abunda zai faru da PDP a babban zaben 2023
- Mai ba da shawara na musamman ga shugaban kasa Muhammadu Buhari kan harkokin yada labarai, Femi Adesina, ya ce PDP za ta kara shan wahala kafin 2023
- Adesina, wanda ya bayyana hakan a ranar Alhamis, 8 ga watan Yuli, a wani rubutu da ya wallafa a shafinsa na Facebook, ya ce jam’iyyar APC mai mulki yanzu amarya ce ga ‘yan siyasar Nijeriya
- Mai magana da yawun shugaban kasar ya kuma lura da cewa fitattun mambobin jam'iyyar adawa da gwamnoni za su koma APC nan ba da dadewa ba
Biyo bayan sauya sheka da wasu gwamnonin jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) da wasu jiga-jigan jam'iyyar suka yi zuwa jam'iyyar All Progressives Congress (APC) mai mulki, fadar shugaban kasa ta ce babbar jam'iyyar adawa ta kasar na iya zama fanko kafin 2023 babban zabe.
Legit.ng ta rahoto cewa mai ba shugaban kasa shawara na musamman kan harkokin yada labarai, Femi Adesina ya bayyana haka a ranar Alhamis, 8 ga watan Yuli, a wani wallafa mai taken, ‘Magana da PDP a harshen da ta fahimta.’
KU KARANTA KUMA: Matasan Sakkwato sun mamaye fadar Sarkin Musulmi akan kalaman batanci ga Annabi
Adesina ya ce ana yi wa PDP magana da yaren da ta fahimta, inda ya kara da cewa tana kururuwar kisan gilla.
Ya ce:
“Abin mamakin shi ne duk lokacin da PDP ke samun nasarori a siyasance, duk abu ne mai kyau. Amma lokacin da take fama da koma baya, to dimokradiyya na fuskantar barazana a kasar."
PDP kururuwa kawai take yi, APC ce za ta ci zaben 2023
Adesina ya bayyana cewa a shekarar 2015, a lokacin da kura ta lafa a babban zabe, APC na da gwamnoni 24 sannan PDP na da 12 yayin da All Progressives Grand Alliance (APGA) ke da guda daya.
KU KARANTA KUMA: Sadu da yaron da ya fara koyon yadda ake tuka jirgi a shekara 7
Ya jaddada:
“Ta hanyar hadewar kawuna, yaduwar abubuwa da fashewa, APC ba ta kula da nasarorinta da kyau ba. Zuwa 2019, yawan gwamnonin ta ya ragu zuwa 19. Kuma PDP ce ta girbe shukan. Amma APC ta sake yin magana, ta daidaita kanta, kuma ta dawo kan hanyoyin cin nasara."
Mai magana da yawun shugaban kasar ya lura cewa Gwamna Dave Umahi na jihar Ebonyi ya koma APC sannan Ben Ayade na jihar Cross River ya bi shi.
Ya lura cewa tare da sauya shekar da Gwamna Bello Matawalle na jihar Zamfara ya yi, jam'iyyar APC tana kara habbaka a bangaren 'yan majalisa da mambobin ta, a matakin tarayya da na jihohi, yana mai cewa wanda ya yi nasara shi ke kwashewa duka yayin da wanda ya fadi yake raguwa.
Adesina ya kara da cewa:
“PDP, a mafi munin gwaninta, tana ihu tana harbawa. Suna washe mu! Dimokiradiyya na cikin hadari! Ashe! Tun yaushe?
"Da yake maraba da Matawalle cikin APC a farkon makon da ya gabata, Shugaba Buhari ya ce jam'iyyar ta kara samun karbuwa 'saboda irin rawar gani da take takawa da kuma jajircewa ga kyakkyawan shugabanci.”
'Yan Najeriya sun maida martani kan sakon Adesina
Ba da daɗewa ba, aka hango 'yan Najeriya a cikin ɓangaren sharhi suna faɗar ra'ayinsu.
Robert Obasi ya ce 'yan baya ne za su yi hukunci kuma duk waɗanda suka yi kuskure za su girbi abun da suka shuka.
Chikawa ya yi addu’a ga Adesina
Utibe Udoka ya bayyana wallafar a matsayin wasiƙar mara ma'ana
Ni ba yar jam’iyyar APC bace, Hadimar Buhari Lauretta Onochie ta bayyanawa Majalisa
A wani labarin kuma, hadimar shugaban kasa, Muhammadu Buhari, kan kafafen yada labaran zamani, Misis Lauretta Onochie, ta bayyanawa kwamitin majalisar dattawa cewa ita ba ’yar jam’iyyar APC ko PDP bace.
Onochie wacce ta kasance yar gani kashenin Shugaba Buhari ta fadawa majalisar cewa ba tada jam’iyyar siyasa.
Ta bayyana hakan ne yayinda ta bayyana gaban majalisar ranar Alhamis domin tantanceta matsayin sabuwar kwamishana a hukumar gudanar da zabe ta kasa watau, INEC.
Asali: Legit.ng