Da Ɗuminsa: Ƙasar Kenya ta magantu kan kama Nnamdi Kanu shugaban IPOB

Da Ɗuminsa: Ƙasar Kenya ta magantu kan kama Nnamdi Kanu shugaban IPOB

  • Gwamnatin Kenya ba ta da masaniya kan cewa wai a Kenya aka kama Nnamdi Kanu shugaban kungiyar IPOB
  • Muteshi, shugaban hukumar shige da fice na Kenya ya ce babu sunan Nnamdi Kanu cikin wadanda suka shigo kasar ta hallastaciyar hanya
  • Muteshi ya kara da cewa ba zai iya sani ba idan Nnamdi Kanu ya shigar kasar Kenya ne ta haramtaciyyar hanya

Shugaban hukumar shige da fice na kasar Kenya, Alexander Muteshi, ya musanta cewa ya san da batun kama Nnamdi Kanu shugaban IPOB da kuma dawo da shi Nigeria, Daily Trust ta ruwaito.

An kama Kanu ne a karshen makon da ta gabata sannan aka taso keyarsa a jirgin sama zuwa Abuja a ranar Lahadi.

Shugaban IPOB, Nnamdi Kanu
Shugaban IPOB, Nnamdi Kanu. Hoto: News Wire
Asali: UGC

An gurfanar da shi gaban Mai shari'a Binta Nyako na babban kotun tarayya da ke Abuja a ranar Talata inda ta umurci hukumar tsaron farin kaya DSS ta ajiye shi har zuwa ranar 26 ga watan Yulin 2021.

Gwamnatin tarayyar Nigeria ba ta ce komai ba game da inda aka kama Nnamdi Kanu.

Sai dai cikin wata sanarwa da Kingsley Kalu, kanin shugaban na IPOB ya fitar a ranar Laraba ya yi ikirarin a Kenya aka kama Kanu kamar yadda The Cable ta ruwaito.

Ya ce:

"A yayin da ya kai ziyara Kenya, an kama Kanu aka tsare shi sannan aka mika shi da hukumomin Nigeria suka dawo da shi Nigeria."
"Gwamnatocin Nigeria da Kenya sun keta hakkin dan uwana. Sun saba doka. Kama mutum a mika shi ga wata kasa babban laifi ne."

Abin da gwamnatin Kenya ta ce game da kama Nnamdi Kanu

Amma yayin hirar da ya yi da The Nation, wata jarida a Kenya a ranar Alhamis, Muteshi ya ce bai da tabbas cewa a Kenya aka kama Kanu.

Amsar da Muteshi ya bawa Nation game da kama Kanu:

"Ba zan iya sani ba."
"Ban san ya shigo kasar nan ba. Zan iya sani idan wani ya shigo kasar ne kawai ta hallastaciyar hanya."

Ba a sani ko Kanu ya shiga Kenya ba bisa ka'ida ba.

Ana tuhumar shugaban na IPOB ne da laifin cin amanar kasa kafin ya tsere bayan an bashi beli.

Kanu ya cigaba da ingiza magoya bayansa ta hanyar kafafen watsa labarai kamar Radio Biafra da dandalin sada zumunta.

Ya kuma kafa wata kungiyar tsaro mai suna ESN da ake zargin tana kai wa hukumomin gwamnati da mutane hari.

Sunday Igboho ya yi 'mi'ara koma baya' kan yin gangamin Yarbawa a Legas

A wani labarin daban, Sunday Igboho, mai ikirarin kare hakkin Yarbawa, ya sha alwashin yin gangamin ƙasar Yarbawa da shi da mabiyansa suka shirya yi a Legas a ranar Asabar, Daily Trust ta ruwaito.

Igboho ya sanar da dakatar da gangamin a ranar Laraba bayan da jami'an hukumar DSS suka kai samame gidansa a Ibadan a ranar Laraba.

Amma wani sako na kai tsaye da ya fitar ta shafin Facebook a ranar Alhamis, Igboho ya ce za a yi gangamin kamar yadda The Nation ta ruwaito.

Asali: Legit.ng

Online view pixel