Da Duminsa: Sunday Igboho ya yi 'mi'ara koma baya' kan yin gangamin Yarbawa a Legas

Da Duminsa: Sunday Igboho ya yi 'mi'ara koma baya' kan yin gangamin Yarbawa a Legas

  • Dan gwagwarmaya mai rajin kare hakkin Yarbawa Sunday Igboho ya ce babu wanda ya isa ya hana gangamin Legas
  • Hakan na zuwa ne bayan Igboho ya sanar da dakatar da yin gangamin da aka shirya yi a Legas a jiya Laraba
  • Sai dai a wani abu mai kama da mi'ara koma baya, Sunday Igboho ya sanar da mabiyansa a ranar Juma'a cewa za a yi gangamin ranar Asabar

Sunday Igboho, mai ikirarin kare hakkin Yarbawa, ya sha alwashin yin gangamin ƙasar Yarbawa da shi da mabiyansa suka shirya yi a Legas a ranar Asabar, Daily Trust ta ruwaito.

Igboho ya sanar da dakatar da gangamin a ranar Laraba bayan da jami'an hukumar DSS suka kai samame gidansa a Ibadan a ranar Laraba.

Sunday Igboho
Da Duminsa: Sunday Igboho ya yi 'mi'ara koma baya' kan gangamin Yarbawa ta Legas. Hoto: Sunday Igboho fans
Asali: UGC

KARANTA WANNAN: 'Dan Majalisar PDP ya bayyana halin da Gwamnan Zamfara Bello Matawalle zai tsinci kansa a 2023

Amma wani sako na kai tsaye da ya fitar ta shafin Facebook a ranar Alhamis, Igboho ya ce za a yi gangamin kamar yadda The Nation ta ruwaito.

Ya yi magana ne ta bakin Olayomi Koiki, mai magana da yawunsa.

Ya ce:

"Ina son tabbatar muku a hukumance cewa gangamin da aka shirya yi a Legas zai faru kamar yadda aka shirya duk da jita-jitar da kuke ji."
"Za a yi gangamin ranar 3 ga watan Yuli kamar yadda aka shirya. An kammala shiri kuma babu abin da ya canja.
"Na yi magana da masu tsara gangamin, zuwa yanzu babu abin da ya canja. Ranar 3 ga watan Yuli misalin ƙarfe 9 na safe. Ana cigaba da shirin da tsarin."
"Na yi magana da babban sakatare na Ilana Omo Odua, George Akinola kuma na yi magana da Bnji Akinyoye kuma yana aiki tukuru don ganin an sako wadanda aka kama.

KU KARANTA:

"Gangamin lumana za mu yi a Legas, babban gangami za mu yi, kada ku damu da abin da ya faru. Abubuwa da dama sun faru a gidan Sunday Igboho.
"Akwai yiwuwar mu fitar da bidiyo daga wurin Sunday Igboho game da gangamin na Legas, da za mu iya fitarwa nan da awa 24, muna shawara kan hakan."

Ya kara da cewa:

"Shi (Igboho) ya ce in fada muku cewa kada ku karaya game da abin da ya faru, har yanzu yana nan daram bai yi watsi da batun kafa kasar Yarbawa ba."

Rundunar yan sanda ta gargadi Igboho ya kiyayi Legas tana mai cewa ƴan daba suna shirin yin kutse su lalata gangamin.

Hotunan Bindigu, Guraye, Layu da sauran kayan tsibbu da DSS ta samu a gidan Igboho yayin nemansa ruwa a jallo

Rahoton da The Guardian ta wallafa ya nuna cewa Hukumar yan farin kaya DSS tana farautar dan gwagwarmayar mai neman kafa kasar Yarbawa da aka fi sani da Sunday Igboho ruwa a jallo.

Hukumar ta DSS ta sanar da hakan ne a daren ranar Alhamis 1 ga watan Yuli yayin taron manema labarai inda ta tabbatar cewa tawagar jami'an tsaro sun kai samame gidan Igboho da ke Soka a Ibadan, jihar Oyo.

An fahimci cewa cewar yan sandan sirrin na Nigeria sun tabbatar da cewa sun bindige mutum biyu cikin masu aiki tare da Igboho yayin da sauran aka ci galaba a kansu aka kama su kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164

Tags: