Hotunan Bindigu, Guraye, Layu da sauran kayan tsibbu da DSS ta samu a gidan Igboho yayin nemansa ruwa a jallo

Hotunan Bindigu, Guraye, Layu da sauran kayan tsibbu da DSS ta samu a gidan Igboho yayin nemansa ruwa a jallo

  • Hukumar yan farin kaya DSS ta fara neman dan gwagwarmayar mai neman kafa kasar Yarbawa da aka fi sani da Sunday Igboho ruwa a jallo
  • Yan sandan sirin na Nigeria, a ranar Alhamis, 1 ga watan Yuli sun tabbatr da cewa sun bindige mutum biyu cikin masu aiki tare da Igboho a gidansa da ke Ibadan, jihar Oyo
  • DSS, yayin taron manema labarai da ta kira ta yi holen a kalla mutane 12 da ta kama tare da bindigu, makamai da layu da guraye da wasu kayan da ta kama a gidansa

Rahoton da The Guardian ta wallafa ya nuna cewa Hukumar yan farin kaya DSS tana farautar dan gwagwarmayar mai neman kafa kasar Yarbawa da aka fi sani da Sunday Igboho ruwa a jallo.

Hukumar ta DSS ta sanar da hakan ne a daren ranar Alhamis 1 ga watan Yuli yayin taron manema labarai inda ta tabbatar cewa tawagar jami'an tsaro sun kai samame gidan Igboho da ke Soka a Ibadan, jihar Oyo.

Hukumar DSS na neman Sunday Igboho ruwa a jallo: Photo credit: Sunday Igboho fans
Hukumar DSS na neman Sunday Igboho ruwa a jallo: Photo credit: Sunday Igboho fans
Asali: UGC

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

An fahimci cewa cewar yan sandan sirrin na Nigeria sun tabbatar da cewa sun bindige mutum biyu cikin masu aiki tare da Igboho yayin da sauran aka ci galaba a kansu aka kama su kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Peter Afunanya, mai magana da yawun hukumar DSS yayin taron manema labaran a Abuja ya yi holen a kalla mutum 12 (11 maza, mace1) da aka kama yayin samamen.

Kayayyakin da DSS ta gano a gidan Sunday Igboho

Wasu daga cikin kayayyakin da aka gano a gidan dan gwagwarmayar na Yarbawa sun hada da guraye, layu, makamai, wayoyin salula, fasfo da sauransu.

Hotunan Bindigu, Guraye da Layu da sauran kayan tsibbu da DSS ta samu a gidan Sunday Igboho
Hotunan Bindigu, Guraye da Layu da sauran kayan tsibbu da DSS ta samu a gidan Sunday Igboho. Hoto: Daily Trust
Asali: Facebook

Hotunan Guraye, Layu da sauran kayan tsibbu da DSS ta samu a gidan Igboho.
Hotunan Guraye, Layu da sauran kayan tsibbu da DSS ta samu a gidan Igboho. Hoto: Daily Trust
Asali: Facebook

Hotunan Bindigu, Guraye, Layu da sauran kayan tsibbu da DSS ta samu a gidan Sunday Igboho
Hotunan Bindigu, Guraye, Layu da sauran kayan tsibbu da DSS ta samu a gidan Sunday Igboho. Hoto: Daily Trust
Asali: Facebook

Hukumar ta ce a halin yanzu Igboho ya tsere amma Afunanya ya shawarce shi ya mika kansa domin babu shakka gwamnati za ta gano shi.

An Yi Awon Gaba da Matar Sunday Igboho Bayan Kame Nnamdi Kanu

Matar mai fafutukar kare hakkin Yarbawa, Sunday Adeyemo da aka fi sani da Sunday Igboho, ta shiga hannun ‘yan bindiga da suka kai hari gidansa da safiyar ranar Alhamis.

Wannan na zuwa ne kamar yadda shugaban kungiyar gamayyar kungiyoyin cin gashin kai na Yarbawa, Ilana Omo Oodua, Emeritus Farfesa Banji Akintoye ya fada.

Ya fadi haka ne a wata sanarwa da ya sanya wa hannu da kansa kuma Manajan Sadarwar kungiyar, Mista Maxwell Adeleye ya gabatar wa manema labarai, Punch ta ruwaito.

Asali: Legit.ng

Online view pixel