Jihohi 10 har Yanzu Sun Gaza baiwa maaikatansu mafi Karancin Albashi

Jihohi 10 har Yanzu Sun Gaza baiwa maaikatansu mafi Karancin Albashi

  • Kungiyar kwadugo ta bayyana wasu jahohi da sukai kunnen uwar shegu wurin biyan mafi karanci albashi
  • Wasu jihohi sun samu lambar yabo dangane dakokarin biyan mafi karancin albashi
  • Jihohi da suka zaftare albashi bayan kin biyan mafi karancin albashi sun sabawa doka

Shekaru biyu bayan Gwamnatin Tarayya ta aminta da sabon mafi karancin albashin, har yanzu akwai jihohi 10 ba su fara aiwatar da shi ba, in ji Kungiyar Manyan Ma’aikatan Najeriya (ASCSN).

Jihohin sun hada da Imo, Benue, Anambra, Kano, Bauchi, Kebbi, Kogi, Nasarawa, Taraba da Zamfara.

Kungiyar kwadagon ta dauki alwashin kin amincewa da rashin biyan giratuti ga ma’aikata, lura da cewa dokar gyaran Fansho ta 2014 ba ta dakatar da biyan giratuti ba.

DUBA NAN: Ya kamata a kara farashin wutan lantarki a Najeriya, yayi arha da yawa: Bankin Duniya

Jihohi 10 har Yanzu Sun Gaza baiwa maaikatansu mafi Karancin Albashi
Jihohi 10 har Yanzu Sun Gaza baiwa maaikatansu mafi Karancin Albashi

KU KARANTA: Na gina gida da daukar nauyin ‘ya’yana 15 - Dattijon da ya shekara 51 yana sana'ar sayar da jarida

A wani taron tattaunawa a daya gudan a Legas, Shugaban Kungiyar Kwamared Tommy Etim Okon, Ya ce Anambra da Taraba sun kammala yarjejeniyar su amma har yanzu ba su aiwatar da shi ba, rahoton TheNation.

Jihohin dake tattaunawa har yanzu

Ya ce Bauchi, Benue, Kebbi, Kogi, Nasarawa da Zamfara suna ci gaba da tattaunawa akan yarjejeniyan yayin da Imo ba ta yi yunkurin yin komai ba.

Ya yaba wa jihohin da suka kammala tattaunawa don aiwatar da mafi karancin albashin, yana mai cewa jihar Kano ba wai karancin albashi kawai ta hana ba, Hadda rage albashin ma’aikata.

Okon ya ce baya kan tsari ga Gwamnati ta rage albashi ko ta yi tunanin kin biya wanda yake a tsarin doka.

Ya ce kungiyan kwadagon ta gaji da tsarin da ake bi a masana'antu da kuma yarjejeniyar gama gari kuma zai dauki hukunci mai tsauri ga jihohin da ba su da karfi.

Ya yi tir da matakin bai-daya da Gwamnatin Jihar Ekiti ta dauka na rage albashin ma’aikata ba tare da tuntubar kungiyar kwadago ba.

Yace: “Mafi karancin albashi doka ce, saboda haka, babu yadda za ayi mu yi yarejeniya da kowane Gwamna don rage albashi. Abin da Gwamnan Jihar Ekiti ya yi ya saba ma doka kuma ba za mu yarda da shi ba. Nan bada jimawa ba zamu kaddamar; a yanzu haka muna iya kokarinmu a kan duk dalila da ya gabatar kuma za mu tabbatar da cewa babu gaskiya a ciki.

Asali: Legit.ng

Online view pixel