Buhari na da ikon tsawaita wa'adin babban sufetan 'yan sanda, kotu ta raba gardama

Buhari na da ikon tsawaita wa'adin babban sufetan 'yan sanda, kotu ta raba gardama

  • Kotu ta bayyana cewa shugaban kasa na da idon tsawaita wa'adin babban sufetan yan sanda
  • Wani lauya mai suna Maxwell Opara ne ya yi karar Shugaba Muhammadu Buhari saboda tsawaita wa'addin tsohon IGP Adamu Mohammed
  • Kotun ta ce kundin tsarin mulki da dokar yan sanda ta bawa shugaban kasa damar tsawaita wa'adin sufetan yan sandan

Babban kotun tarayya da ke zamanta a Abuja ta jadada ikon da shugaban kasa ke da shi na tsawaita wa'adin mulkin babban sufetan yan sanda, IGP, har zuwa lokacin da aka kama shirin nada sabo, The Cable ta ruwaito.

A ranar 4 ga watan Fabrairu, Shugaba Muhammadu Buhari ya tsawita wa'adin Babban Sufetan Yan sanda Mohammed Adamu ta watanni uku bayan ya cika shekarunsa na aiki 35 a ranar 1 ga watan Fabrairu.

Shugaba Buhari da Mukadashin IGP, Alkali Usman
Shugaba Muhammadu Buhari da Mukadashin IGP, Alkali Usman. Hoto: The Cable
Asali: Facebook

DUBA WANNAN: 'Yan bindigan da suka kai hari Makarantar Kebbi sun harbi ɗalibai biyu, Shaida

Bayan hakan, wani lauya mai suna Maxwell Opara, ya shigar da shugaban kasa kara a kotu yana mai cewa sashi na 215 da 7 na kudin tsarin mulkin Nigeria karkashin dokokin yan sanda na 2020 ya ce Adamu ba zai iya cigaba da aiki a matsayin IGP ba bayan lokacin ritayarsa.

The Nation ta ruwaito cewa a yayin kare kansa, IGP ya shaidawa kotun cewa sabon dokar na yan sanda ya bashi wa'adin shekaru hudu da zai kare a 2023 ko 2024.

Shugaba Buhari da Ministan Shari'a Abubakar Malami - wadanda suna cikin wadanda aka yi kararsu - sun shaidawa kotun ta bakin lauyansu cewa doka ta bawa IGP damar cigaba da rike mukaminsa har zuwa 2023 ko 2024.

KU KARANTA: 2023: Fastocin neman takarar shugabancin ƙasa na Yahaya Bello sun mamaye Abuja

Hukuncin da kotu ta yanke

A yayin da ya ke yanke hukuncin a ranar Juma'a, Ahmed Mohammed, lauyan da ke shari'ar ya ce tunda dokar yan sanda da kundin tsarin mulki ya bawa shugaban kasa damar nada IGP, hakan ya bashi damar tsawaita wa'adin IGP da zai yi murabus kafin ya gama tattaunawa da kwamitin koli na yan sanda da wasu hukumomin kafin ya nada wanda zai maye gurbinsa.

Alkalin ya kuma bayyana cewa doka bata ce komai ba kan ko shugaban kasa zai iya tsawaita wa'adin babban sufetan yan sanda da zai yi murabus.

Tuni dai an nada Alkali Usman Baba a matsayin mukadashin babban sufetan yan sanda.

Asali: Legit.ng

Online view pixel