2023: Fastocin neman takarar shugabancin ƙasa na Yahaya Bello sun mamaye Abuja

2023: Fastocin neman takarar shugabancin ƙasa na Yahaya Bello sun mamaye Abuja

  • Fastocin takarar shugaban kasa a 2023 na Gwamna Yahaya Bello sun bayyana a jihar Abuja
  • Kungiyar Nigeria Youth Awareness Group ta dade tana yi wa Gwamna Yahaya Bello kamfen na takarar shugaban kasa
  • Amma dai har yanzu gwamnan na jihar Kogi bai fito a fili ya sanar da cewa zai yi takarar shugaban kasar ba

Fastocin kamfen na neman takarar shugabancin kasa na gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello sun mamaye manyan tituna a babban birnin tarayya, Abuja kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Wannan shine na baya bayan a cikin fastocin yakin neman zaben shugabancin kasa da aka gani a titunan Abuja a yan makonnin da suka gabata.

Fastocin takarar shugaban kasa na Yahaya Bello
Fastocin kamfen din takarar shugabancin kasa na Gwamna Yahaya Bello a Abuja. Hoto: Daily Trust
Asali: Facebook

DUBA WANNAN: Rashin tsaro: Mazauna wasu unguwanni a Zaria sunyi Sallar Al-Ƙunuti kan 'yan bindiga

Wasu daga cikin masu fatan neman kujerar tsayawa takarar shugabancin kasar a zaben 2023 da aka ga fastocinsu a Abuja sun hada da jagoran jam'iyyar APC na kasa, Bola Ahmed Tinubu, Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar da tsohon shugaban majalisar dattijai, Bukola Saraki.

Fastocin na Yahaya Bello na dauke da rubutu daban-daban kamar, 'Shugabancin Kasa na 2023; Yahaya Bello yana goyon bayan canji, Yahaya Bello domin shugaban kasa na 2023'.

An lika fastocin a wurare daban-daban da suka hada da shataletale, manyan gadoji na sama, sandunan wutar lantarki da sauransu.

KU KARANTA: Dakatar da Twitter ya hana wa gwamnonin PDP kafar yaɗa labaran ƙarya, Fadar Shugaban ƙasa

An gano fastocin kusa da Ma'aikatar Shari'a; Sakatarriyar Gwamnatin Tarayya; NICON Luxury; Sheraton Hotel da titin da tafi zuwa sakatariyar jam'iyyar All Progressives Congress (APC) na kasa; Hukumar Kula da Jami'o'i na Kasa, NUC; Shataletalen Maitama da Garki 2.

Kungiyar wayar da kan matasa ta NYAG 2023 ta dade tana yi wa Bello kamfen duk da cewa har yanzu bai sanar a hukumance cewa zai yi takarar na shugaban kasa ba.

A wani labarin, kun ji cewa an kashe wani jami'in dan sanda sannan an sace wasu yan kasar China su hudu da ke aiki a layin dogo na Legas zuwa Ibadan kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Wakilin majiyar Legit.ng ya ruwaito cewa yan bindigan sun labe ne a kan iyakar Adeaga/Alaagba wani gari da ke kan iyakar jihohin Oyo da Ogun a ranar Laraba.

Mazauna wasu unguwanni a Zaria sunyi Sallar Al-Ƙunuti kan 'yan bindiga Yan bindigan sanye da bakaken kaftani sun kutsa wurin da ake aikin layin dogon a kauyen Adeaga/Alaagba da ke karamar hukumar Odeda a jihar Ogun.

Asali: Legit.ng

Online view pixel