Da Ɗuminsa: 'Yan bindigan da suka kai hari Makarantar Kebbi sun harbi ɗalibai biyu, Shaida

Da Ɗuminsa: 'Yan bindigan da suka kai hari Makarantar Kebbi sun harbi ɗalibai biyu, Shaida

  • Wani shaidan gani da ido ya tabbatar da cewa yan bindigan da suka kai hari makarantar sakandare ta Yauri a jihar Kebbi sun harbi dalibai biyu
  • Shaidan ya ce sun harbi wani dalibi na miji a mazaunansa sannan sun kuma harbi wata daliba mace a hannunta
  • Shaidan ya kara da cewa yan bindigan sun tafi da malamai uku ko hudu ciki har da mataimakiyar shugaban makarantar

Yan bindigan da suka kai hari kwallejin gwamnatin tarayya da ke Birnin Yauri, jihar Kebbi, sun harbi dalibai biyu a cewar wani shaidan gani da ido, rahoton Daily Trust.

Shaidan wanda ya nemi a sakaya sunansa ya shaidawa majiyar Legit.ng cewa yan bindigan sun sace maza da mata.

Taswirar Jihar Kebbi
Taswirar Jihar Kebbi. Hoto: Channels TV
Asali: Facebook

KU KARANTA: An kama matar da ta damfari ɗan siyasa N2.6m da sunan za a yi amfani da 'iskokai' a taimaka masa ya ci zaɓe

Sun kuma yi awon gaba da malamai hudu ciki har da mace da mataimakiyar shugaban makarantar.

Information Nigeria ta ruwaito cewa shaidan ya kara da cewa, yan bindigan da suka kawo hari misalin karfe 12.30 sun yi musayar wuta da jami'an yan sanda.

Ya cigaba da cewa yan sandan sun fara musayar wuta da su a kofar shiga makarantar, amma wasu daga cikin yan bindigan suka kutsa suka shiga da bayan makarantar, da shigarsu suka faa harbe-harbe.

Ya ce

"An sace malamai uku ko hudu daga makarantar, cikin wadanda aka sace akwai mataimakiyar shugaban makarantar da kuma malama mace."
"Yan bindigan sun harbi dalibai biyu, namiji da mace. Sun harbi na mijin a mazaunansa yayin da ita kuma macen ta samu rauni a hannunta."

A wani labarin, kun ji cewa an kashe wani jami'in dan sanda sannan an sace wasu yan kasar China su hudu da ke aiki a layin dogo na Legas zuwa Ibadan kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Wakilin majiyar Legit.ng ya ruwaito cewa yan bindigan sun labe ne a kan iyakar Adeaga/Alaagba wani gari da ke kan iyakar jihohin Oyo da Ogun a ranar Laraba.

Mazauna wasu unguwanni a Zaria sunyi Sallar Al-Ƙunuti kan 'yan bindiga Yan bindigan sanye da bakaken kaftani sun kutsa wurin da ake aikin layin dogon a kauyen Adeaga/Alaagba da ke karamar hukumar Odeda a jihar Ogun.

Asali: Legit.ng

Online view pixel