Hauhawar tattalin arziki: Nau'ukan kayan abinci Guda 5 da suka fi tsada a kasuwa yanzu

Hauhawar tattalin arziki: Nau'ukan kayan abinci Guda 5 da suka fi tsada a kasuwa yanzu

  • Kayan abinci yayi masifar tsada amma a hakan akwai masarufin da tsadar su ta musamman ne
  • Duk sanda mutum ya ziyarci Kasuwa zai iya gama yawo ya dawo batare daya siya wani abu ba duba da yadda abubuwa suka hauhawa
  • Farashin masarufin dasuka fi kowanne tsada sun hada da Tumatir Naman kaza Garin kwaki da sauransu

Farashin kayan abinci a Najeriya yayi masifar tashin Gauron zabi amma akwai farashin wasu kayan Masarufin da su kayi Matukar bada Mamaki

Duk sanda Mutum ya ziyarci kasuwa. Zaka ji dan kasuwa na korafin "komai yayi tsada ya kara kudi fa", kuma haka abun yake.

Zuwa Kasuwa domin siyan wani abu ze iya sa mutum ya je ya dawo bai sayi komai ba.Tsadan Rayuwa,a Nijeriya ya yi tsanani.

Akwai wata sabuwar sara da Matasan Najeriya suka kirkiro wai 'Sapa' Yana nuna yanda kudi sukayi wahalar Samu amma kuma dole a kashe.

Ga jerin kayan Masarufi biyar da suka fi kowan ne tsada;

1. Markadadden Tumatir

Markadaden Tumatir ya kasance wani nau'i ne na Tumatiri da mutum ze siya a lokacin da baida kudin siyan kwalon tumatiri. Amma a yanzu sai attajiri ne ke iya siyan wanan tumaturin, Inda yayi tashin gauron zabi daga Naira Hamsin zuwa dari da Hamsin wani wuri har Dari Biyu.

2. Garin Kwaki

Shima wanan nau'i ne na abinci da mutum ka iya siya a lokacin da ya ke halin ha'ula'i, Zaka sayi gwangwani a abunda bai gaza Naira Hamsin ba amma a yanzu ya dawo Naira Dari Shida.

3. Agada (Plantain)

Wani mai wasan Kwaikwayo Mai suna Mofe Duncan ya rubuta cewa ya sayi kwarya Agada Naira 6000. Abun ya matukar ba ma mutane dariya, Dan bai dade ba da ake saida kwaryan Dubu daya amma a yanzu idan anyi maka sauki shine a saida maka Dubu Biyar.

KU KARANTA: Alheri kan alheri: Ma’aurata ’yan Najeriya sun samu ’yan biyu shekara 21 suna jiran haihuwa

Hauhawar tattalin arziki: Nau'ukan kayan abinci Guda 5 da suka fi tsada a kasuwa yanzu
Hauhawar tattalin arziki: Nau'ukan kayan abinci Guda 5 da suka fi tsada a kasuwa yanzu

KU DUBA: Ana mini barazanar kisa, Shugaban Hukumar EFCC Abdulrashid Bawa

4. Kifi (Sardine)

Cikin nau'ikan kifaye da ake sayarwa a kasuwa yanzu, Kifi Sardine ya yi tashin gwauron zabo inda wasu ke cewa "cin Sardine yanzu sai wane da wane". A baya ana samun mai matsakaicin girma a N500, amma yanzu N900

5. Naman Kaji

A da zaka iya samun rabin kilon naman kaza a Naira 650, Amma a yanzu bai gaza Kasa da 1800 Zuwa 2000 ba.

Shinkafa kam dama ta dade da zama Hajiya babba saboda tayi tsada tun farkon kafa wannan Gwamnati inda aka rufe kan iyaka.

Asali: Legit.ng

Online view pixel