Matukin jirgin da yayi hatsari an saka ranar aurensa, zai angwance da masoyiyarsa

Matukin jirgin da yayi hatsari an saka ranar aurensa, zai angwance da masoyiyarsa

- Taiwo Olufemi Asaniyi, daya daga cikin matukan jirgin da yayi hatsari an saka ranar bikinsa

- Kamar yadda abokansa biyu suka bayyana, zai angwance ne da masoyiyarsa a watan Oktoba

- Sun sanar da yadda yake ta shirin bikinsa kuma har shagalin saka rana an yi kafin nan

Taiwo Olufemi Asaniyi, matukin jirgin saman sojoji da yayi hatsari a ranar Juma'a ya shirya aurensa da masoyiyarsa a watan Oktoba mai zuwa.

Asaniyi, Ibrahim Attahiru, da wasu sojoji tara sune a jirgi kirar Beechcraft 350 da yayi hatsari kusa da filin sauka da tashin jiragen sama na Najeriya dake Kaduna.

A wata wallafa da Adedeji Adeniyi, abokin mamacin yayi a Twitter, yace a cikin kwanakin nan ne suka tattauna shirin bikinsa kafin mummunan al'amarin ya faru.

Kamar yadda yace, matukin jirgin zai auri wata shakikiyar kawarsa ne kafin mutuwarsa.

KU KARANTA: Gwamnatin Nasarawa ta bai wa sarakunan gargajiya motoci sama da Naira miliyan 800

Matukin jirgin da yayi hatsari an saka ranar aurensa, zai angwance da masoyiyarsa
Matukin jirgin da yayi hatsari an saka ranar aurensa, zai angwance da masoyiyarsa. Hoto daga @ChannelsTV
Asali: Twitter

"Femi na shirin aurensa a watan Oktoba. Mun yi magana a kan masu kida da komai a makon nan. Zai aura wata shakikiyar kawarsa ne. Shi ya tuka jirgin a jiya. Ubangiji ya jikanka Flt LT TO Asaniyi. Duk wanda ya mutu a jirgin Ubangiji yasa ya huta," ya rubuta.

Wani abokin Asaniyi ya nuna firgicinsa a kan aukuwar lamarin inda yace mamacin ya saka shi a matsayin babban aboki a aurensa mai zuwa.

"Asaniyi ne ya tuka jirgin. Muna ta shirin bikinsa, ni ne zan zama babban aboki," ya wallafa.

Ya kara da wallafa bidiyon sa ranar mamacin tare da wacce zai aura wanda aka yi a watan Maris.

KU KARANTA: 'Yan bindiga sun kai hari kan iyakar Neja da ke kusa da Abuja, sun sace mutum 12

A wani labari na daban, Shugaban kwamitin majalisar dattawa kan al'amuran sojin kasa, Sanata Ali Ndume na jam'iyyar APC daga yankin Borno ta kudu, ya kwatanta mutuwar shugaban sojin kasa, Laftanal Janar Ibrahim Attahiru da ibtila'in da ya fadawa kasar nan kuma yace ya rasu a matsayin jarumi.

A wata takarda da yasa hannu da kansa a ranar Asabar, Sanatan yace labarin mutuwar Attahiru da sauran sojin goma ya matukar girgiza shi, Vanguard ta ruwaito.

Ndume ya jajanta yadda marigayin zakakurin sojan ya rasu a lokacin da kasar nan ta zuba masa ido domin kawo sauyi tare da ganin bayan ta'addanci da duk wani nau'in laifuka a Najeriya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel