Mutuwar Attahiru ibtila'i ce ga kasa, ya rasu a matsayin jarumi, Ndume
- Shugaban kwamitin majalisar dattawa na sojin kasa, Ali Ndume, ya nuna jimaminsa na rasuwar COAS Attahiru da tawagarsa
- Ndume wanda sanata ne mai wakiltar mazabar Borno ta kudu, yace mutuwar Attahiru Ibtila'i ne ga kasa kuma ya rasu a jarumi
- Sanatan yace rashin ba ga iyalansu bane kadai, ga dukkan Najeriya ne balle a lokacin da ake fama da rashin tsaro
Shugaban kwamitin majalisar dattawa kan al'amuran sojin kasa, Sanata Ali Ndume na jam'iyyar APC daga yankin Borno ta kudu, ya kwatanta mutuwar shugaban sojin kasa, Laftanal Janar Ibrahim Attahiru da ibtila'in da ya fadawa kasar nan kuma yace ya rasu a matsayin jarumi.
A wata takarda da yasa hannu da kansa a ranar Asabar, Sanatan yace labarin mutuwar Attahiru da sauran sojin goma ya matukar girgiza shi, Vanguard ta ruwaito.
Ndume ya jajanta yadda marigayin zakakurin sojan ya rasu a lokacin da kasar nan ta zuba masa ido domin kawo sauyi tare da ganin bayan ta'addanci da duk wani nau'in laifuka a Najeriya.
KU KARANTA: Muhimman abubuwa 5 da baku sani ba game da kungiyar ISWAP
Ya kwatanta Attahiru da sauran tawagarsa da 'yan kasa masu sadaukarwa da kishi wadanda tuni suka fara amfani da tsarikan shawo kan matsalar tsaro ciki da wajen Najeriya dake zama kalubale ga zaman lafiyan kasar.
Ndume yayi fatan gafara ga rayukan wadanda suka rasa rayukansu yayin hatsarin jirgin saman. Ya kara da addu'ar juriya da hakuri ga iyalan wadanda suka rasu.
Ndume yace: "Babu shakka, wannan rashi ne ga dukkan sojin Najeriya a wannan lokacin da suke tunkarar rashin tsaro a dukkan sassan kasar nan. Ina fatan Allah mai daukaka da ya baiwa iyalansu da sojin Najerya juriya da hakurin wannan rashin. Ameen."
KU KARANTA: Yadda Labarin mutuwar Shekau ya jefa mazauna Maiduguri nishadi da hamdala
A wani labari na daban, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya shiga matukar damuwa a kan hatsarin jirgin sama da yayi ajalin shugaban dakarun sojin kasa, Laftanal Janar Ibrahim Attahiru da wasu manyan sojoji.
Kamar yadda mai magana da yawun shugaban kasa, Malam Garba Shehu ya wallafa a shafinsa na Twitter, ya bayyana alhinin da shugaban kasan ya shiga.
"A yayin addu'a ga Ubangiji da ya gafartawa rayukan masu kishin kasan, shugaban kasan yace wannan babban rashi ne yayin da dakarun sojin kasar nan suka zage wurin ganin karshen kalubalen tsaron da kasar nan ke fuskanta," Shehu ya wallafa.
Asali: Legit.ng