Da duminsa: Sojoji sun mamaye unguwar Oshodi kan rahoton kisan wani Soja

Da duminsa: Sojoji sun mamaye unguwar Oshodi kan rahoton kisan wani Soja

Hankalin jama'a ya tashi yayinda fasinjoji suka gaza wucewa sakamakon mamaye unguwar Oshodi da jami'an hukumar Sojin Najeriya suka yi da safiyar Alhamis, 20 ga Mayu, 2021.

Daily Trust ta tattaro cewa Sojojin sun dira unguwar ne saboda kisan wani jami'in hukumar Sojin sama da wasu matasa suka kashe a unguwar.

Sojojin na lallasa mutane, yayinda suka lalata motocin haya.

Wasu mazaunan dake yunkurin zuwa wuraren aikinsu sun gaza zuwa yayinda dalibai suka koma gida.

Yan kasuwa sun gudu daga shagunansu yayinda direbobin motocin haya sun gudu sun bar motocinsu.

Sojojin na farautar yan tada zauna tsaye dake unguwar.

DUBA NAN: Shugabannin PDP sun shiga ganawa kan sauya shekar gwamnan Kross Ribas

DUBA NAN: Wannan abin takaici ne - PDP ta yi martani cikin fushi kan ficewar gwamna Ayade zuwa APC

A bangare guda, shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, ranar Alhamis, ya ƙaddamar da sabbin jiragen yaƙi guda uku da gwamnatinsa ta siyo wa rundunar sojin sama (NAF).

Shugaban ya miƙa jiragen ne a sansanin sojin dake Makurɗi yayin bikin cikar NAF shekaru 57 da kafuwa.

Shugaba Buhari, wanda ministan tsaro, Bashir Magashi, ya wakilta yace jiragen yaƙin JF-17 da aka ƙara zuwa kayan aikin NAF zasu taimaka sosai wajen yaƙin da rundunar take yi da yan ta'adda, yan bindiga da sauran manyan laifuka da ƙasar ke fama dasu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel