Da duminsa: Shugabannin PDP sun shiga ganawa kan sauya shekar gwamnan Kross Ribas
- Jam'iyyar PDp ta girgiza bisa sauya shekar gwamnanta zuwa APC
- Daga 2019 zuwa yanzu PDP ta yi rashin gwamnoni 2 a kudu
- Jamiyyar ta yi kira ga sauran yan PDP dake jihar su hada kawunansu
Kwamitin gudanarwan uwar jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) ta shiga ganawar gaggawa a hedkwatar jam'iyyar dake Abuja sakamakon sauya shekarar gwamnan jihar Korss Ribas, Ben Ayade, daga PDP zuwa APC.
Leadership ta ruwaito cewa mambobin kwamitin sun taru a ofishin shugaban jam'iyyar gabanin ganawar gaggawan.
Kakakin jam'iyyar PDP, Kola Ologbondiyan, bayan ganawa ya saki jawabi da 'yayan jam'iyyar cewa su kwantar da hankulansu kuma su zama tsintsiya madaurinki guda.
Yace: "Jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) ta samu labarin sauya shekan gwamnan Cross River, Farfesa Ben Ayade."
"Jam'iyyar na kira ga masu ruwa da tsaki da mabiyanta dake jihar Kross Roba su hada kansu kuma su tabbatar da cewa komai na yadda ya kamata."
Mun kawo muku cewa gwamnan jihar Kross Ribas, Ben ayade, ya sauya sheka daga jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) zuwa jam'iyyar All Progressives Congress (APC).
Gwamna Ayade ya sanar da hakan ne da safiyar Alhamis a ganawar da yayi da gwamnonin APC shida da suka kai masa ziyara gidan gwamnatin jihar.
KU KARANTA: Wannan abin takaici ne - PDP ta yi martani cikin fushi kan ficewar gwamna Ayade zuwa APC
DUBA NAN: Gwamna El-Rufai ya yi wa Gwamnoni kaca-kaca, NGF ta bukaci a koma saida litar fetur N408:
Ben Ayade, gwamnan jihar Cross Rivers ya bukaci sauran gwamnoni a tsohuwar jam'iyyarsa ta Peoples Democratic Party, PDP, su dawo jam'iyyar All Progresives Congress, APC.
"Akwai bukatar mu hada hannu da Shugaba Buhari a kokarinsa na inganta da habbaka lamuran kasar nan. Ina kira ga sauran gwamnoni su yi koyi da ni su fahimci dalili na na shiga APC," Ayade ya ce.
"Ya kamata mu yi aiki tare da shugaban kasa domin cigaba da hadin kan Nigeria. Akwai bukatar dukkan mu mu zauna tare da Shugaban kasa a teburi daya mu ceci Nigeria."
Asali: Legit.ng