Wannan abin takaici ne - PDP ta yi martani cikin fushi kan ficewar gwamna Ayade zuwa APC

Wannan abin takaici ne - PDP ta yi martani cikin fushi kan ficewar gwamna Ayade zuwa APC

- Shugaban shiyyar kudu maso kudu na PDP ya ce ficewar Ayade abin kaico ne

- Ficewar Ayade ta zo wa ‘yan Najeriya da dama a bazata

Jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) tayi tir da sauya shekar da gwamna Ben Ayade ya yi zuwa jam'iyyar All Progressives Congress (APC).

Shugaban jam’iyyar na kudu maso kudu, Dan Orbih, ya ce abin takaici ne da bakin ciki cewa gwamnan jihar Kuros Riba ya yanke shawarar shiga jam’iyyar da ta jefa miliyoyin ‘yan Nijeriya a kangin rayuwa.

KU KARANTA KUMA: Da duminsa: Shugabannin PDP sun shiga ganawa kan sauya shekar gwamnan Kross Ribas

Wannan abin takaici ne - PDP ta yi martani cikin fushi kan ficewar gwamna Ayade zuwa APC
Wannan abin takaici ne - PDP ta yi martani cikin fushi kan ficewar gwamna Ayade zuwa APC Hoto: @senatorbenayade
Asali: Twitter

Orbih a wata tattaunawa ta wayar tarho da Vanguard ya yi tambaya game da dalilin da ya sa Ayade ya yanke shawarar barin jam'iyyar da a cikinta ne ya ci zaben gwamna.

Jigon na PDP ya yi kira da a samar da dokokin da za su tilasta wa ‘yan siyasar da ke rike da mukaman siyasa su sauka daga kan kujerunsu idan suka sauya sheka.

Ya ce:

"Lokaci ya yi da 'yan majalisar za su fito fili su bayyana wannan. Ba zai yiwu ka shiga inuwar wata jam’iyya zuwa nasara ba sannan ka juya ka dauke nasarar zuwa wata jam’iyyar ba.

“Ya kamata a zo da wata doka da za ta fito karara ta bayyana cewa idan zababben shugaba zai bar jam’iyyar da aka zabe shi a cikinta, ya kamata ya bar mukaminsa. Wannan zai taimaka wajen tsabtace siyasarmu."

KU KARANTA KUMA: Jerin lokuta biyar da aka rahoto cewa Shugaban Boko Haram Shekau ya mutu

A wani labarin, Ben Ayade, gwamnan jihar Cross Rivers ya bukaci sauran gwamnoni a tsohuwar jam'iyyarsa ta Peoples Democratic Party, PDP, su dawo jam'iyyar All Progresives Congress, APC, Daily Trust ta ruwaito.

Legit.ng ta ruwaito yadda Ayade ya sauya sheka daga jam'iyyar na PDP ya koma jam'iyya mai mulkin kasa wato APC.

Gwamnan na Cross Rivers ya yi jawabi ne a gidan gwamnati da ke Calabar inda ya yi taro da shugabannin jam'iyyar APC.

Asali: Legit.ng

Online view pixel