Bayan makonni 3 da tafiya hutu, mutan Borno na farin cikin dawowan gwamna Zulum

- Zulum ya dawo bakin aiki bayan hutun makonni uku

- Ya dawo da albishir na dauka Malamai da ma’aikatan lafiya aiki

- Al’ummar jihar Borno sun cika sun banbatse da farin cikin dawowan Gwamnansu

Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, ya koma bakin aiki bayan makonni da daukam hutu inda yaje kasa mai tsarki don ibada.

Zulum, ya dira Maiduguri ne da ranar Laraba, bisa jawabin da hadiminsa ya saki.

Gabanin tafiyarsa, Zulu, ya mika ragamar mulki ga mataimakinsa, Usman Umar Kadafur.

Zulum ya samu kyakkyawan tarba daga dubban jama’a wanda suka hada da ma’aikatan gwamnati, shugabannin jam’iyya, masoya da abokan arziki.

Dirarsa ke da wuya, Zulum ya tabbatarwa al’ummarsa cewa gwamnatinsa zata cigaba da kokarin samar da zaman lafiya domin farfado da kasuwanci da noma.

Hakazalika ya yi alkawarin daukan sabbin Malaman makaranta da ma’aikatan asibiti aiki.

Mun kawo muku rahoton cewa Zulum ya tafi hutu ne ranar 29 ga Afrilu, 2021.

Bayan makonni 3 da tafiya hutu, mutan Borno na farin cikin dawowan gwamna Zulum
Bayan makonni 3 da tafiya hutu, mutan Borno na farin cikin dawowan gwamna Zulum Hoto: The Governor of Borno State
Asali: Facebook

DUBA NAN: Duk wadanda suka rufe kasuwanci da sunan yajin aiki zasu dandana kudarsu

Bayan makonni 3 da tafiya hutu, mutan Borno na farin cikin dawowan gwamna Zulum
Bayan makonni 3 da tafiya hutu, mutan Borno na farin cikin dawowan gwamna Zulum Hoto: The Governor of Borno State
Asali: Facebook

DUBA NAN: NLC Ta Janye Yajin Aikin Da Ta Tsunduma a Kaduna

Bayan makonni 3 da tafiya hutu, mutan Borno na farin cikin dawowan gwamna Zulum
Bayan makonni 3 da tafiya hutu, mutan Borno na farin cikin dawowan gwamna Zulum Hoto: The Governor of Borno State
Asali: Facebook

Asali: Legit.ng

Online view pixel