El-Rufai: Duk wadanda suka rufe kasuwanci da sunan yajin aiki zasu dandana kudarsu

El-Rufai: Duk wadanda suka rufe kasuwanci da sunan yajin aiki zasu dandana kudarsu

- Gwamna Nasir El-Rufai na jihar Kaduna yace duk wadanda suka rufe kasuwancin a jihar zasu gane kurensu

- Kamar yadda Gwamnan yace, kungiyar kwadago na da ikon yin yajin aiki amma ba tare da rufe wuta da hana siyar da man fetur ba

- Gwamnan yace abinda kungiyar tayi ya sabawa shari'a kuma zagon kasa ne ga tattalin arzikin jiharsa

Gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai, ya ce wadanda suka katse kasuwanci a jihar da sunan yajin aiki zasu dandana kudarsu.

A cikin kwanakin da suka gabata, mambobin kungiyar kwadago ta kasa da El-Rufai sun yi artabu a kan hukuncin gwamnatin jihar na sallamar sama da ma'aikata 4,000 a jihar.

A sakamakon hakan, kungiyar kwadago karkashin shugabancin Ayuba Wabba ta shiga yaji aikin kwanaki biyar wanda ta fara a ranar Litinin, The Cable ta ruwaito.

KU KARANTA: Tsohon rasit ya nuna cewa kakan Dangote na cikin 'yan Najeriya na farko da suka fara saka kudi a banki

El-Rufai: Duk wadanda suka rufe kasuwanci da suna yajin aiki zasu dandana kudarsu
El-Rufai: Duk wadanda suka rufe kasuwanci da suna yajin aiki zasu dandana kudarsu. Hoto daga @TheCableng
Asali: UGC

KU KARANTA: Hotunan gidan Obafemi Awolowo sun bar jama'a baki bude cike da mamaki

Wannan hukuncin bai yi wa El-Rufai dadi ba wanda ya bayyana cewa yana neman Wabba da sauran 'yan kungiyar kwadagon ruwa jallo a kan abinda ya kwatanta da zagon kasa ga tattalin arziki.

A yayin cigaba da bayani a kan wannan lamarin , Gwamnan jihar Kaduna da ya halarci taron shekara na haraji wanda CITN ta shirya a Kaduna, yace tabbas hakkin kungiyar ne su yi zanga-zanga amma kuma ba wai su hana kasuwanci tafiya ba.

"Akwai kokarin da suka yi na hana halastattun kasuwanci budewa. Akwai kokarin hana bankuna budewa da kuma hana gidajen man fetur siyarwa. Wannan laifi ne kuma ba shari'a bace kuma zamu dauka mataki," yace.

"Ba mu sukar yajin aikinsu, suna da damar yajin aiki amma ka bar ma'aikatarsa za ta iya aiki ko babu kai.

"Baku da ikon hana kasuwanci budewa kuma zamu dauka mummunan mataki a kan mutanen da suka yi hakan."

A wani labari na daban, duk da ikirarin da gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari ke yi na cewa ta ci galaba a kan 'yan ta'addan Boko Haram kuma ta kwace yankin arewa maso gabas, bayanan da ake samu daga wasu gwamnoni abun tsoro ne.

Ministan yada labarai da al'adu na kasa, Lai Mohammed a 2019 ya ce dakarun sojin kasar nan cike da nasara sun ci galaba kan mayakan Boko Haram. Ya ce Najeriya na fuskantar sabon salon rashin tsaro ne wanda ya zama ruwan dare dama duniya.

Sai dai a halin yanzu akwai jihohin da ke fama da hare-hare wanda ake zargin na 'yan ta'addan Boko Haram ne ke kaiwa, Premium Times ta ruwaito.

Asali: Legit.ng

Online view pixel