Da Dumi-Dumi: NLC Ta Janye Yajin Aikin Da Ta Tsunduma a Kaduna
- Kungiyar kwadago ta Najeriya ta dakatar da yajin aikin da ta tsunduma a jihar Kaduna a makon nan
- Kungiyar ta sanar da dakatarwar ne ta bakin shugabanta, Ayuba Wabba da yammacin Laraba
- Kungiyar ta yi takun saka da gwamnan jihar Kaduna Nasir El-Rufai biyo bayan korar ma'aikata
NLC ta dakatar da yajin aikin gargadi na kwanaki 5 a Kaduna, Shugaban NLC, Ayuba Wabba ya sanar da shawarar, ya ce ya yi hakan ne don girmama gayyatar da FG ta yi don sasanta rikicin da ke tsakanin kungiyar kwadagon da gwamnatin jihar Kaduna, in ji TVC
Channels Tv ta ruwaito cewa, a safiyar yau, Ministan kwadago da samar da ayyukan yi, Sanata Chris Ngige ya shiga cikin takun-saka tsakanin gwamnatin jihar Kaduna da kungiyoyin kwadago ta hanyar gayyatar bangarorin biyu zuwa taron sasantawa.
Ngige ya umarci bangarorin biyu da su ci gaba da kasancewa a yadda suke har zuwa lokacin da za a sasanta batutuwan.
KU KARANTA: Yanzu-Yanzu: Jami'an EFCC Na Sake Rantsuwar Aiki da Gaskiya Tsakani da Allah
“Don haka ina amfani da karfi na a matsayin Ministan kwadago da samar da aikin yi, a karkashin dokar rigingimun kasuwanci, CAP. T8, Dokokin Tarayyar Najeriya (LFN) 2004; in gayyace ku tare da manyan jami’anku zuwa taron sasanta rikicin cikin gaggawa,” inji shi.
Tsoma bakin Ngige na zuwa ne kwanaki uku bayan NLC ta fara zanga-zanga biyo bayan sallamar ma’aikatan gwamnati sama da dubu bakwai da gwamnatin jihar Kaduna ta yi.
Yajin aikin ya durkusar da mahimman fannoni na tattalin arziki a jihar.
Gwamnan jihar Nasir El-Rufai a martaninsa ya bayyana Shugaban NLC da sauran shugabannin kungiyoyin kwadagon da neman zagon kasa ga tattalin arziki da kai hare-hare kan ababen more rayuwa a jihar Kaduna a karkashin Dokar Laifuka iri daban-daban.
KU KARANTA: Wabba: El-Rufai Ya Yi Hayar 'Yan Daba Cike Da Manyan Motoci 50 Su Fatattaki NLC
A wani labarin, Kamfanin rarraba wutar lantarki a jihar Kaduna, Kaduna Electric ya sake bai wa abokan huldarsa hakuri game da rashin wuta a jihar tsawon kwana hudu sakamakon yajin aikin kungiyar kwadago ta Najeriya (NLC).
A makon nan jihar Kaduna ta rikice da zanga-zanga biyo bayan korar wasu ma'aikata da gwamnatin jihar ta yi, lamarin da ya tunzura dubban jama'a.
Kungiyar kwadago ta Najerita (NLC) ta tsundumawa yajin aiki sakamakon korar abokan aikinsu, lamarin da ya jawo cece-kuce tsakanin gwamnatin jihar Kaduna da kungiyar kwadagon.
Asali: Legit.ng