Yanzu-yanzu: Yan daba sun mamaye ofishin kungiyar kwadagon Najeriya dake Kaduna

Yanzu-yanzu: Yan daba sun mamaye ofishin kungiyar kwadagon Najeriya dake Kaduna

- Har yanzu ana cigaba da zanga-zanga da yajin aiki a jihar Kaduna

- Yan kungiyar kwadago sun ce wajibi ne gwamnatin Kaduna ta sauko daga shawarar sallamar ma'aikata

- Gwamnatin jihar kuma ta ce sam ba zata fasa korar dubunnan ma'aikata ba

Wasu yan daba sun mamaye ofishin kungiyar kwadagon Najeriya NLC dake jihar Kaduna.

Yan daban rike da makamai kimanin 100 sun mamaye sakatariyar ne inda yan kungiyar kwadagon ke tattare don gudanar da zanga-zanga.

Amma, jami'an yan sanda sun dakile yan bangan kuma an damke kimanin 20 cikinsu, Daily Trust ta ruwaito.

Kakakin hukumar yan sandan jihar, ASP Muhammad Jalige, ya tabbatar da wannan labari inda yace an tura jami'ai kwantar da kuran.

Jiya mnun kawo muku rahoton cewa wasu yan daba sun sun kaiwa masu zanga-zangan kwadago hari a shataletalen NEPA dake cikin birnin jihar.

Yan daban na adawa da yan kungiyar kwadagon dake yajin aiki sakamakon koran ma'aikata 7000 da gwamnatin jihar tayi.

KU KARANTA: Tsohon sirikin Shugaba Buhari ya magantu a kan nemansa da ICPC ke yi

Yanzu-yanzu: Yan daba sun mamaye ofishin kungiyar kwadagon Najeriya dake Kaduna
Yanzu-yanzu: Yan daba sun mamaye ofishin kungiyar kwadagon Najeriya dake Kaduna
Asali: Original

DUBA NAN: El-Rufai: Duk wadanda suka rufe kasuwanci da sunan yajin aiki zasu dandana kudarsu

A bangare guda, gwamnatin tarayya ta gayyaci gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasiru El-Rufa'i, da shugabannin NLC zuwa wajen taron gaggawa data shirya domin yin sulhu a tsakanin su, kamar yadda Vanguard ta ruwaito.

Gwamnatin ta sanya ranar Alhamis 20 ga watan Mayu domin tattaunawar sulhu tsakanin ɓangarorin biyu a babban Birnin tarayya Abuja.

Wannan na cikin ƙoƙarin da gwamnatin tarayya ke yi domin dakatar da yajin aiki da kuma rikicin dake tsakanin gwamnatin Kaduna da ƙungiyar kwaduga kan sallamar ma'aikata a jihar Kaduna.

Asali: Legit.ng

Online view pixel