Tsohon sirikin Shugaba Buhari ya magantu a kan nemansa da ICPC ke yi
- Tsohon sirikin shugaban kasa Buhari, Gimba Kumo, ya ce hukumar ICPC bata taba gayyatarsa ba
- Kumo ya koka da yadda ICPC ta bayyana cewa tana neman ruwa jallo bayan bata taba aiko masa da goron gayyata ba
- Ya tabbatar da cewa hukumar tsaro da farin kaya da EFCC ta bincikesa kuma tuni aka tura rahoton wurin shugaba Buhari
Gimba Kumo, tsohon sirikin shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce bai taba samun gayyata daga hukumar yaki da rashawa mai zaman kanta (ICPC) ba kafin ta ce tana nemansa a kan badakalar kudi har $65 miliyan yayin da yake manajan daraktan bankin gidaje na tarayya.
Kumo ya sanar da hakan a wata wasika da ya rubuta zuwa shugaban ICPC, Farfesa Bolaji Owasanoye mai kwanan wata 18 ga Mayun 2021.
A ranar Alhamis da ta gabata ne hukumar ICPC tace tana neman Kumo ruwa a jallo tare da Tarry Rufus da Bola Ogunsola a kan wata damfara da ake zarginsu da ita, jaridar The Punch ta ruwaito.
A takardar da mai magana da yawun hukumar ICPC, Azuka Ogugua yasa hannu, yayi kira ga jama'a da su samar da bayanan inda mutanen uku suke.
KU KARANTA: Gwamna ya fatattaki kwamishinoni 25, shugaban ma'aikatansa da sakataren gwamnati
KU KARANTA: Da duminsa: 'Yan bindiga sun kutsa kotu, sun yi awon gaba da alkali a Katsina
Kumo ya ce ICPC ta take dokarta na bayyana cewa tana nemansa ruwa jallo ba tare da ta bi hanyar da ta dace ba.
Ya kara da cewa tuni hukumar tsaro ta farin kaya da hukumar yaki da rashawa da hana yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa ta EFCC suka bincikesa kuma aka turawa shugaban kasa Buhari rahoton.
A wani labari na daban, duk da ikirarin da gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari ke yi na cewa ta ci galaba a kan 'yan ta'addan Boko Haram kuma ta kwace yankin arewa maso gabas, bayanan da ake samu daga wasu gwamnoni abun tsoro ne.
Ministan yada labarai da al'adu na kasa, Lai Mohammed a 2019 ya ce dakarun sojin kasar nan cike da nasara sun ci galaba kan mayakan Boko Haram. Ya ce Najeriya na fuskantar sabon salon rashin tsaro ne wanda ya zama ruwan dare dama duniya.
Sai dai a halin yanzu akwai jihohin da ke fama da hare-hare wanda ake zargin na 'yan ta'addan Boko Haram ne ke kaiwa, Premium Times ta ruwaito.
Asali: Legit.ng