Da Ɗumi-Ɗumi: FG Ta Gayyaci Gwamnan Kaduna da Ayuba Waba, Ta Bayyana Ranar da Zasu Yi Taron Sulhu

Da Ɗumi-Ɗumi: FG Ta Gayyaci Gwamnan Kaduna da Ayuba Waba, Ta Bayyana Ranar da Zasu Yi Taron Sulhu

- Gwamnatin tarayya ta gayyaci gwamnatin Kaduna da shugabannin ƙungiyar ƙwadugo zuwa wajen taron sulhu a Abuja

- FG ta shirya taron ne a ƙoƙarin da take yi na samar da maslaha a tsakanin ɓangarorin biyu

- Za'a yi taron ranar Alhamis 20 ga watan Mayu a ofishin ministan ƙwadugo na ƙasa dake babban birnin tarayya, Abuja

Gwamnatin tarayya ta gayyaci gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasiru El-Rufa'i, da shugabannin NLC zuwa wajen taron gaggawa data shirya domin yin sulhu a tsakanin su, kamar yadda Vanguard ta ruwaito.

KARANTA ANAN: Zan Hukunta Ku Yadda Ba Zaku Sake Sha’awar Dawowa Kaduna Ba, El-Rufai Ga Shugabannin NLC

Gwamnatin ta sanya ranar Alhamis 20 ga watan Mayu domin tattaunawar sulhu tsakanin ɓangarorin biyu a babban Birnin tarayya Abuja.

Da Ɗumi-Ɗumi: FG Ta Gayyaci Gwamnan Kaduna da Ayuba Waba, Ta Bayyana Ranar da Zasu Yi Taron Sulhu
Da Ɗumi-Ɗumi: FG Ta Gayyaci Gwamnan Kaduna da Ayuba Waba, Ta Bayyana Ranar da Zasu Yi Taron Sulhu Hoto: vanguardngr.com
Asali: UGC

KARANTA ANAN: Tashin Hankali, An Tsinci Gawarwakin Wasu Yan Fulani Makiyaya Biyu a Ƙauyen Abuja

Wannan na cikin ƙoƙarin da gwamnatin tarayya ke yi domin dakatar da yajin aiki da kuma rikicin dake tsakanin gwamnatin Kaduna da ƙungiyar kwaduga kan sallamar ma'aikata a jihar Kaduna.

Gwamnatin ta gayyaci ɓangarorin biyu ne ta ofishin ministan kwadugo, Chris Ngige, domin ta shiga tsakani, kamar yadda The Nation ta ruwaito.

An shirya yin zaman sulhun ne da misalin ƙarfe 11:00 na safe a ofishin ministan kwadugo na ƙasa ranar Alhamis a Abuja.

Waɗanda aka gayyata zuwa wajen taron sulhun sun haɗa da; Gwamnan Kaduna, Malam Nasir El-Rufa'i tare da manyan jami'an gwamnatinsa, da kuma shugaban NLC, Ayuba Waba, tare da manyan shugabannin ƙungiyar.

A wani labarin kuma Jami'an Kwastam Sun yi Ram da Ƙwayoyin Turamol Katan 1,387 a Jihar Rivers

Hukumar kwastam ta ƙasa ta damƙe katan ɗin kwayar turamol guda 1,387 a cikin wasu kayayyaki a jihar Rivers.

Kakakin runduna ta biyu dake yankin tashar jirgin ruwa dake Onne a jihar ne ya bayyana haka a Patakwal.

Asali: Legit.ng

Online view pixel