Kada ku nuna imani wajen ragargazan yan kungiyar IPOB, Sifeto Janar ga Yan sanda

Kada ku nuna imani wajen ragargazan yan kungiyar IPOB, Sifeto Janar ga Yan sanda

- Hukumar yan sanda ta kaddamar da sabon atisayen a kudancin Najeriya

- An shirya bikin kaddamar da atisayen ne a birnin Enugu

- An yi rashin jami'an yan sanda da dama a yankin kudu maso gabashin Najeriya

Sifeto Janar na yan sanda, Usman Alkali Baba, ya yi kira ga jami'ansa dake yankin kudu maso gabas cewa kada su ragawa yan kungiyar IPOB masu rajin ballewa daga Najeriya.

Ya ce wajibi ne yan sandan su zage dantse wajen yakan yan kungiyar saboda irin barazanar da suke yiwa rayuwan yan sanda da jama'an gari.

Alkali ya bada wannan umurni ne ranar Talata, lokacin da ya kaddamar da atisaye na musamman mai suna "‘Operation Restore Peace’ (Operation RP) " a yankin Igbo, rahoton The Nation.

A cikin shekarar nan, yan ta'addan IPOB/ESN sun kai munanan hare-hare ofishohin yan sanda da gidajen yari.

Hakan ya yi sanadiyar mutuwar jami'an yan sanda da kama tare da guduwan yan gidan yari.

KU DUBA: Shugaba Buhari ya yi sabbin nade-nade masu muhimmanci guda biyu

Kada ku nuna imani wajen ragargazan yan kungiyar IPOB, Sifeto Janar ga Yan sanda
Kada ku nuna imani wajen ragargazan yan kungiyar IPOB, Sifeto Janar ga Yan sanda Credit: Presidency
Asali: Facebook

KU KARANTA: EFCC ta damke Soja, da wasu mutum 33 kan laifin Yahoo-yahoo

Sifeto Janar ya umurci yan sandan suyi abubuwa guda biyu; na farko a samar da zaman lafiya a yankin kudu maso gabas, na biyu kuma a yi hakan cikin kwarewa ba tare da saba doka ba.

IGP ya bukaci yan sanda su bi a hankali wajen hulda da farin huka kuma kada su ci zarafinsu.

A cewarsa: "Wannan yaki a shekarun baya na fuskantar matsalolin garkuwa da mutane, fashi da makami, da kuma rikicin kabilu. Wannan abu ne da yan kungiyar IPOB da mayakansu ESN ke yi."

"Yan kungiyar masu rajin ballewa daga Najeriya sun dau sabon salon kai hare-hare kan yan siyasa, jami'an yan sanda, Sojoji, da wasu hukumomin tsaro a yankin."

A rahoton Leadership, wannan atisaye zai gudana ne tare da gudunmuwar Sojoji, hukumomin leken asiri, da sauran hukumomin tsaro.

Ya kara da cewa, "Mun fadawa jami'an da aka tura su kasance masu bin doka amma kada su ragawa yan ta'adda ko kadan."

Asali: Legit.ng

Online view pixel