EFCC ta damke Soja, da wasu mutum 33 kan laifin Yahoo-yahoo

EFCC ta damke Soja, da wasu mutum 33 kan laifin Yahoo-yahoo

Jami'an hukumar hana almundahana da yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa wato EFCC sun yi ram da yan damfarar yanar gizo wadanda aka fi sani da Yahoo-yahoo guda 34 a jihar Osun.

Daga cikin wadannan mutanen akwai jami'in Soja, Adebisi Jamiu, wanda ya gudu daga bakin aiki.

Hukumar ta damke wadannan matasa ne a simamen da ta kai da maraicen Talata, 18 ga Mayu, 2021 birnin Osogbo, jihar Osun.

EFCC ta bayyana hakan ne a jawabin da ta saki da yammacin Talata a shafinta na Tuwita .

EFCC ta damke Soja, da wasu mutum 33 kan laifin Yahoo-yahoo
EFCC ta damke Soja, da wasu mutum 33 kan laifin Yahoo-yahoo Hoto: @officialEFCC
Asali: Twitter

"An damke tsohon Sojan mai shekaru 22, Jamiu da sauran ne bayan labarin leken asirin na cewa suna aiki yahoo-yahoo," EFCC tace.

"Sauran sun hada Muritala Olaniyi Lateef, Wasiu Olajide, Wasiu Sadiq, Olaniran Abiodun, Ayodeji Tosin, Olaniran Tayo, Oginni Oluwaseun, Oginni Olatunde, Ojuade Oluwafemi da Ibrahim Wande."

Hakazalika akwai Oladiran Olayinka, Akinjobi Akinwunmi, Abayomi Aderohunmi, Olaoluwa Temitope, Idowu Olawale, Lawrence Taiwo, Ojo Gbenga, Tiamiyu Farouk, Oladele Seun, Akiniyi Boluwatife, Olaoluwa Mutiu, Olakunle Omolofe, Olalere Samad, Edbadon Johnson, Oketunbi Kayode, Gbeyide Tomiwa, Oluwanisola Elmuqsit, Bathlomew John, Ibikunle James, Olamide Oluwaseyi, Yusuf Mohammed, Adebola Ibrahim, da Ajayi Muyiwa.

Hukumar ta ce za a gurfanar da su a kotu bayan kammala bincike kansu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel