Da duminsa: Shugaba Buhari ya yi sabbin nade-nade masu muhimmanci guda biyu

Da duminsa: Shugaba Buhari ya yi sabbin nade-nade masu muhimmanci guda biyu

- Duk da yana Faransa, Shugaba Buhari bai daina ayyukansa na gida ba

- Shugaban kasan ya tafi wakiltar Najeriya a taron alakar Afrika da Faransa

- Ya amince da nadin sabbin Diraktocin ma'aiktar NDE da Kwalejin NILS

Shugaba Muhammadu Buhari ya amince da nadin Mallam Abubakar Nuhu Fikpo matsayin Dirakta Janar na ma'aikatar samar da aikin yi watau NDE.

Hakazalika Buhari ya nada Kwamred Issa Aremu a matsayin Dirakta Janar da Kwalejin Kwadago na kasa (NILS).

Sakon shugaban kasan na kunshe cikin jawabin da mai magana da yawunsa, Malam Garba Shehu, ya saki da yammacin Talata.

"Shugaba Muhammadu Buhari ya amince da nadin Mallam Abubakar Nuhu Fikpo matsayin tabattacen Dirakta Janar na Ma'aikatar samar da aiki NDE," Shehu yace.

"Gabanin nadinsa, Malam Fikpo ya kasance mukaddashin Diraktan ma'aikatar."

"Hakazalika shugaba Buhari ya nada Kwamred Issa Aremu matsayin Diraktan Kwalejin Kwadago na kasa (NILS)."

"Wa'adin nadin na shekaru hudu ne fari daga ranar 18 ga Mayu, 2021."

KU KARANTA: El-Rufa'i yace masu zanga-zanga tamkar yan bindiga ne, ya sallami Malaman jami'ar KASU da suka shiga

Da duminsa: Shugaba Buhari ya yi sabbin nade-nade masu muhimmanci guda biyu
Da duminsa: Shugaba Buhari ya yi sabbin nade-nade masu muhimmanci guda biyu Hoto: Presidency
Asali: Twitter

DUBA NAN: El-Rufai ya sha alwashin koran ma'aikatan da suka yi zanga-zanga da NLC

A bangare guda, gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufa'i, ya alanta neman shugaban kungiyar kwadagon Najeriya NLC, Kwamred Ayuba Wabba, da sauran shugabannin da suka shiga jihar zanga-zanga ruwa a jallo.

El-Rufa'i ya yi alkawarin bayar da kyautar kudi ga duk wanda ya san inda wadannan shugabannin kwadago suke boye.

Ya tuhumcesu ne da laifin fito-na-fito da tattalin arzikin jihar Kaduna kuma hakan ya sabawa doka.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng