Da Ɗumi-Ɗumi: Yan Bindiga Su Hallaka Sojoji Biyu, Sun Yi Awon Gaba da Wani Ɗan China

Da Ɗumi-Ɗumi: Yan Bindiga Su Hallaka Sojoji Biyu, Sun Yi Awon Gaba da Wani Ɗan China

- Wasu yan bindiga sun kai sabon hari ƙauyen Nasko dake ƙaramar hukumar Magama a jihar Neja

- Jami'an soji sun maida martani ga yan bindigan inda akai ɗauki ba daɗi a tsakaninsu, biyu daga cikin sojojin sun rasa rayuwarsu

- Anyi musayar wuta tsakanin jami'an soji da yan bindigan, amma daga baya yan bindigan suka tsere zuwa cikin daji

A ranar Litinin, wasu yan bindiga sun kashe jami'an soji biyu tare da sace wani ɗan China a ƙaramar hukumar Magama jihar Neja, kamar yadda the nation ta ruwaito.

KARANTA ANAN: Amurka Ta Damƙe Wani Nakusa da Gwamnan Ogun Bisa Zargin Sace Dala Dubu $350,000

Rahotanni sun bayyana cewa yan bindigan sun kai hari ƙauyen Nasko dake ƙaramar hukumar Magana, amma sai suka yi arangama da jami'an soji.

Haɗuwar su keda wuya sai aka fara musayar wuta a tsakanin sojojin da kuma yan bindigan.

Da Ɗumi-Ɗumi: Yan Bindiga Su Hallaka Sojoji Biyu, Sun Yi Awon Gaba da Wani Ɗan China
Da Ɗumi-Ɗumi: Yan Bindiga Su Hallaka Sojoji Biyu, Sun Yi Awon Gaba da Wani Ɗan China Hoto: thenationonlineng.net
Asali: UGC

Wata majiya a cikin jami'an tsaro ta bayya cewa sojoji biyu sun rigamu gidan gaskiya a harin yayin da mutane da dama suka jikkata.

Har ila yau, babu wani bayani akan yan bindiga nawa ne aka kashe ko aka raunata a yayin fafatawar, amma a rahoton premium times ya nuna cewa an kashe yan bindiga biyu.

KARANTA ANAN: Matsalar Tsaro: CAN Ta Goyi Bayan Shawarar Tsohon Shugaban Ƙasa IBB, Tace Wannan Ba Shine Karon Farko Ba

Wani mazaunin ƙauyen da lamarin ya faru yace yan bindigan sun tsere zuwa bayan wani dutse 'Dutsen libale' wanda sanannen dutse ne a ƙauyen.

Har ya zuwa yanzun jami'an soji tare da wasu jami'an tsaro sun bi sawun yan bindigan zuwa dajin dake kusa da dutsen.

Yan bindigan sun sami nasarar yin gaba da wani ɗan China, wanda ɗaya ne daga cikin ma'aikatan wani Kamfani dake aikin hanya a yankin.

Da aka tuntuɓi kakakin hukumar yan sanda na jihar Neja, DSP Wasiu Abiodun, domin jin ta bakinsa, bai ɗaga kiran waya ko ya dawo da amsar saƙonnin da aka tura mishi ba.

A wani labarin kuma Mataimakin Shugaban Ƙasa Osinbajo Ya Bayyana Matsayarsa Kan Tsayawa Takara a 2023

Mataimakin shugaban Ƙasa, Farfesa Yemi Osinbajo, ya bayyana matsayarsa a kan takarar shugabancin ƙasar nan bayan kammala wa'adin Buhari.

Mr. Osinbajo yayi watsi da wani shafin yanar gizo da wasu mutane ke ɗaukar nauyi, wanda ke bayyana cewa mataimakin shugaban zai nemi takara a 2023.

Asali: Legit.ng

Online view pixel