Amurka Ta Damƙe Wani Nakusa da Gwamnan Ogun Bisa Zargin Sace Dala Dubu $350,000

Amurka Ta Damƙe Wani Nakusa da Gwamnan Ogun Bisa Zargin Sace Dala Dubu $350,000

- Rahotanni sun bayyana cewa an damke wani na kusa da gwamnan jihar Ogun a ƙasar Amurka bisa zarginsa da satar wasu kuɗaɗe

- An bayyana cewa Abidemi Rufa'i, babban mai taimakawa gwamnan, ya shiga hannu ne a ranar jumu'a da yamma

- Antoni janar na ƙasar yace zasu cigaba da gudanar da bincike don gano duk waɗanda ke da hannu a sace kuɗaɗen tallafi na rage raɗaɗin COVID19

Ƙasar Amurka ta cafke babban mai taimakawa gwamnan Ogun, Dapo Abiodun, da zargin sama da faɗi da dala dubu $350,000 na tallafin marasa aikin yi a ƙasar.

KARANTA ANAN: Twitter Ta Zaɓi Najeriya Domin Gwada Sabon Salon Sakonta Na Murya

An damƙe Abidemi Rufa'i ranar Jumu'a da yamma a filin tashi da saukar jiragen sama JFK dake birnin New York, kamar yadda the cable ta ruwaito.

A jawabin ofishin Antoni Janar na Amurka a Washinton, ya bayyana cewa an shigar da ƙorafi ne a kan Rufa'i da zargin ya sace dala dubu $350,000 kuɗin tallafawa marasa aikin yi daga sashin ɗaukar aiki ESD dake Washinton.

Amurka Ta Damƙe Wani Nakusa da Gwamnan Ogun Bisa Zargin Sace Dala Dubu $350,000
Amurka Ta Damƙe Wani Nakusa da Gwamnan Ogun Bisa Zargin Sace Dala Dubu $350,000 Hoto: thecable.ng
Asali: UGC

A ƙorafin da aka shigar, Rufa'i yayi amafani da bayanan ƙarya na mazauna Washinton sama da 100 wajen shigar da neman tallafi a ESD.

Ana zargin Rufa'i da aikata makamancin wannan laifin a Hawaii, Wyoming, Massachusetts, Montana, New York, da Pennsylvania.

Hakanan an shigar da ƙorafin zargin ɗan Najeriyan da amfani da email guda ɗaya wajen cimma kudirinsa.

Rahoton the nation ya bayyana cewa, Wakilin sashin bincike na Amurka yace an tura sama da dala dubu $288,000 a wani asusun bankin ƙasar Amurka mallakin Rufa'i.

KARANTA ANAN: Matsalar Tsaro: CAN Ta Goyi Bayan Shawarar Tsohon Shugaban Ƙasa IBB, Tace Wannan Ba Shine Karon Farko Ba

Hakanan an gano cewa an tura wasu kuɗaɗen zuwa wasu asusu na daban a Jamaica, New York waɗanda mallakin yan uwan Rufa'i ne.

Yayin da yake martani kan kama Rufa'i lokacin zaman shari'a na farko, muƙaddashin Antonin Amurka, yace sun daɗe suna aiki da tawagar bincike tun watan Afrilu 2020 domin gano masu karkatar da kuɗin da aka ware don tallafawa marasa ƙarfi dake zaune a Amurka.

Yace: "Tunda ofishin mu ya samu rahoton satar kuɗin a watan Afrilu 2020, mun yi aiki tuƙuru tare da wakilan binciki da zartar da doka domin bibiyar waɗanda suka aikata wannan aikin na satar kuɗin tallafi domin rage raɗaɗin annobar COVID19."

"Wannan ba shine na farko ba kuma ba zai zama na karshe ba domin har yanzun muna cigaba da gudanar da bincike a kan lamarin."

Za'a cigaba da shari'ar Rufa'i ranar Laraba yayin da zai cigaba da zama a tsare.

A wani labarin kuma Daga Ƙarshe, Mataimakin Shugaban Ƙasa Osinbajo Ya Bayyana Matsayarsa Kan Tsayawa Takara a 2023

Mataimakin shugaban Ƙasa, Farfesa Yemi Osinbajo, ya bayyana matsayarsa a kan takarar shugabancin ƙasar nan bayan kammala wa'adin Buhari.

Mr. Osinbajo yayi watsi da wani shafin yanar gizo da wasu mutane ke ɗaukar nauyi, wanda ke bayyana cewa mataimakin shugaban zai nemi takara a 2023.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Tags: