Daga Ƙarshe, Mataimakin Shugaban Ƙasa Osinbajo Ya Bayyana Matsayarsa Kan Tsayawa Takara a 2023

Daga Ƙarshe, Mataimakin Shugaban Ƙasa Osinbajo Ya Bayyana Matsayarsa Kan Tsayawa Takara a 2023

- Mataimakin shugaban Ƙasa, Farfesa Yemi Osinbajo, ya bayyana matsayarsa a kan takarar shugabancin ƙasar nan bayan kammala wa'adin Buhari

- Mr. Osinbajo yayi watsi da wani shafin yanar gizo da wasu mutane ke ɗaukar nauyi, wanda ke bayyana cewa mataimakin shugaban zai nemi takara a 2023

- Mataimakin shugaban ya bayyana cewa har yanzun bashi da sha'awar tsayawa takara, ya maida hankali ne kan aikin ofishin sa na yanzu

Ofishin mataimakin shugaban ƙasa yace gasar neman tikitin takarar shugabancin ƙasar nan a zaɓen 2023 yana daɗa jan hankali, kamar yadda Premium Times ta ruwaito.

KARANTA ANAN: Da Ɗuminsa: Rundunar Yan Sanda Ta Damƙe Wani Tsohon Soja Dake Horad da Yan Ta'addan IPOB

Sai dai ofishin ya bayyana cewa mataimakin shugaban ƙasa, Farfesa Yemi Osinbajo, bashi da niyyar yin takarar shugaban ƙasa a yanzu.

Kakakin mataimakin shugaban, Laolu Akande, shine ya faɗi haka a wani jawabi daya fitar yau a babban birnin tarayya Abuja.

Yace Mr. Osinbajo bashi da alaƙa da waɗanda ke yaƙin neman zaɓensa a yanar gizo.

Daga Ƙarshe, Mataimakin Shugaban Ƙasa Osinbajo Ya Bayyana Matsayarsa Kan Tsayawa Takara a 2023
Daga Ƙarshe, Mataimakin Shugaban Ƙasa Osinbajo Ya Bayyana Matsayarsa Kan Tsayawa Takara a 2023 Hoto: @ProfOsinbajo
Asali: Twitter

Akande yace:

"An jawo hankalin ofishin mataimakin shugaban ƙasa kan wani shafin yanar gizo mai suna supportosinbajo.ng, wanda yake kira ga yan Najeriya su shigo tawagar yan sa kai domin nuna goyon bayansu ga Osinbajo yayin da zaɓen 2023 ke gabatowa."

KARANTA ANAN: Yajin Aiki: An Kulle Sakatariyar Gwamnatin Kaduna, Mambobin NLC Sun Mamaye Kan Hanyoyi

"Bayanan wannan shafin yanar gizon da neman agajin da suke yi yana cigaba da jan hankalin masu amfani da dandalin sada zumunta na whatsapp, kuma suna faɗin cewa Osinbajo ya amince zai yi takara amma a ɓoye."

"Ofishin mataimakin shugaban ƙasa bashi da wata alaƙa da wannan shafin yanar gizo ko tawagar mutanen dake ɗaukar nauyin shi, Osinbajo bai nuna sha'awar tsayawa takarar kowace kujera ba a zaɓen 2023."

"Amma ya maida hankali wajen aikinsa na mataimakin shugaba a wannan gwamnatin wajen ƙoƙarin shawo kan duk wani abu daya taso a ƙasa, da kuma kulawa ga yan Najeriya." Inji shi.

Mr. Osinbajo shine abokin takarar shugaban ƙasa Muhammadu Buhari a zaɓen shugaban ƙasa na 2015 da 2019.

A wani labarin kuma Wasu Yan Bindiga Sun Kai Hari Hedkwatar Hukumar Zaɓe INEC, Sun Ƙona Motoci 6

Wasu yan bindiga sun kai hari hedkwatar hukumar zaɓe INEC ta jihar Enugu , inda suka ƙona Motocin Hilux shida dake harabar wajen.

Jami'an tsaro sun samu nasarar fatattakar maharan waɗanda suka yi ƙoƙarin kutsa kai cikin ginin ofishin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262