Matsalar Tsaro: CAN Ta Goyi Bayan Shawarar Tsohon Shugaban Ƙasa IBB, Tace Wannan Ba Shine Karon Farko Ba

Matsalar Tsaro: CAN Ta Goyi Bayan Shawarar Tsohon Shugaban Ƙasa IBB, Tace Wannan Ba Shine Karon Farko Ba

- Ƙungiyar CAN ta goyi bayan shawarar da tsohon shugaban ƙasa a mulkin soja, Ibrahim Badamasi Babangida, ya baiwa gwamnati kan matsalar tsaro

- IBB ya shawarci gwamnatin tarayya data siyo sabbin makamai na zamani sannan ta horad da jami'an tsaro yadda zasu yi amfani da su

- CAN tace wannan shawara ce mai matuƙar kyau, amma wannan ba shine karon farko da aka baiwa FG irinta ba

Ƙungiyar kiristoci CAN, tace shawarar da tsohon shugaban ƙasa a mulkin soja, Ibrahim Badamasi Babangida, ya baiwa gwamnatin tarayya tana da kyau sosai amma wannan ba shine na farko da ka bada irin wannan shawarar ba.

KARANTA ANAN: Daga Ƙarshe, Mataimakin Shugaban Ƙasa Osinbajo Ya Bayyana Matsayarsa Kan Tsayawa Takara a 2023

Legit.ng hausa ta kawo muku rahoton cewa IBB ya shawarci gwamnatin tarayya da ta samarwa jami'an soji makamai na zamani sannan ta horad da su yadda zasu yi amfani da makaman.

CAN ta bayyana cewa yan Najeriya da dama sun taɓa bada irin wannan shawarar amma gwamnati bata ɗaukar ta da muhimmanci.

CAN Ta Goyi Bayan Shawarar Tsohon Shugaban Ƙasa IBB, Tace Wannan Ba Shine Karon Farko Ba
CAN Ta Goyi Bayan Shawarar Tsohon Shugaban Ƙasa IBB, Tace Wannan Ba Shine Karon Farko Ba Hoto: globalpeace.org
Asali: UGC

Mataimakin shugaban CAN a arewacin Najeriya, Rev. John Hayab, shine ya bayyana haka a wata tattaunawa da yayi da wakilin Vanguard.

Yace a baya gwamnatin tarayya tayi kasafi na musamman domin samar da makamai na zamani tare da horad da jami'an soji amma har yanzun ba'a yi komai ba.

Yace: "Maganar gaskiya mafi yawancin makaman da jami'an tsaron ƙasar nan ke amfani dasu tsoffi ne, kuma jami'an nada ƙarancin horo irin na zamani saboda haka akwai buƙatar horad dasu."

"Yan ta'adda da yan bindiga dake kai hare-hare a arewa suna da manyan makamai, sannan suna da isasshen horo akan yadda zasu yi amfani da su fiye da jami'an tsaron ƙasar nan."

KARANTA ANAN: An Hallaka Wani Ɗan Fulani Makiyayi Tare Da Shanu 52 a Wani Sabon Hari a Jihar Plateu

"Shawarar da tsohon shugaban ƙasa IBB ya baiwa gwamnati cewa ta samar wa jami'an tsaro sabbin makamai na zamani kuma a horad dasu tana da kyau, amma wannan ba shine karon farko ba, yan Najeriya da dama sun taɓa bada irinta."

John Hayab ya ƙara da cewa tunda yanzun tsohon shugaban ƙasa a mulkin soja ya ƙara jaddada maganar wata ƙila masu riƙe da madafun iko suyi wani abu.

Yace: "Muna fatan gwamnati tayi wani abu a kan wannan lamarin tunda tsohon shugaban ƙasa yayi magana akai. Duk da an faɗa mana cewa an fitar da kuɗi domin siyo sabbin makamai amma har yanzun ba'a san ina kuɗin suka yi ba."

"A kowanne hali, jami'an sojin mu suna buƙatar goyon bayan mu kamar yadda IBB ya faɗa. Amma yakamata duka matakan gwamnati uku suyi duk me yuwu wa domin su jawo hankalin mutane su sake yarda dasu."

"Domin hakan zaisa yan Najeriya su cigaba da taimakawa jami'an tsaro a yaƙin da suke yi da yan ta'adda."

A wani labarin kuma Babbar Magana: Zama Gwamna Ƙara Talautad Dani Yayi, Inji Tsohon Gwamna

Tsohon gwamnan jihar Imo, Sanata Rochas Okorocha, yace zaman shi gwamna na shekara takwas ƙara talautad dashi yayi.

Sanatan wanda yake wakiltar Imo ta yamma ya faɗi haka ne yayin da yake musanta zargin da ake masa cewa ya mallaki kadarori a Abuja.

Asali: Legit.ng

Online view pixel