An kashe adadi na yan ta'addan Boko Haram da yammacin Talata a harin Maiduguri

An kashe adadi na yan ta'addan Boko Haram da yammacin Talata a harin Maiduguri

Gamayyar Dakarun Sojojin Najeriya da yan sanda sun samu nasarar hallaka adadi na yan ta'addan Boko Haram ranar Talata yayinda sukayi yunkurin shiga cikin birnin Maiduguri, mazauna sun laburta.

A cewar HumAngle, an kwace akalla motar yaki guda da babbar bindiga da babura a hannun yan ta'addan.

Mayakan kungiyar Boko Haram sun cinna wuta a wasu a gidaje a Maiduguri, babban birnin jihar Borno, yayinda ake shirin bude baki ranar Talata.

An kuma ji karar harbin bindiga da abubuwa masu fashewa a sassan birnin daban-daban musamman kusa da Jiddari Polo.

Wani mazauni, Musa Kadai, ya bayyanawa Daily Trust cewa misalin karfe 5:50 na yamma ya fara jin karar harbi.

"Abin kaman mafarki yazo min. Ina shirin bude baki muka fara jin harbe-harbe da tashin bama-bamai. Da wuri na kwashe yara na biyu da matana muka gudu daga unguwar," yace.

"Wannan abin takaici ne... Da mukakoma misalin karfe 8 na dare don buda baki abubuwa sunyi sauki."

An kashe adadi na yan ta'addan Boko Haram da yammacin Talata a harin Maiduguri
An kashe adadi na yan ta'addan Boko Haram da yammacin Talata a harin Maiduguri

Wani jami'in CJTF, Abdul Ba’ Kura, ya ce an hallaka goman yan ta'addan sakamakon ruwan wutan da gamayyar jami'an tsaro tayi musu.

"Sun shigo ta Molai da Judumari. Amma jami'an tsaro sun mayar da martani cikin gaggawa," Abdul yace.

"Allah ya bamu nasara kan Boko Haram jiya. Ina mai tabbatar muku."

Asali: Legit.ng

Online view pixel