Shugaba Muhammadu Buhari ya gana da gwamnonin Arewacin Najeriya
1 - tsawon mintuna
Shugaba Muhammadu Buhari ya gana da kungiyar gwamnonin Arewacin Najeriya karkashin jagorancin gwamnan jihar Plateau, Simon Bako Lalong.
Mai magana da yawun shugaban kasa, Femi Adesina, ya ce anyi wannan zama ne ranar Alhamis a fadar shugaban kasa.
Daga cikin wadanda suka halarci zaman akwai gwamnan jihar Zamfara, Muhammad Bello Matawalle; gwamnan jihar Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal; da gwamnan jihar Kaduna, Nasir Ahmed El-Rufa'i.
Sauran sune gwamnan jihar Kwara, AbdulFatah Ahmed; gwamnan jihar Kebbi, Atiku Bagudu; da gwamnan jihar Nasarawa; Injiniya Abdullahi Sule.
Asali: Legit.ng