An garƙame hedkwatar kamfanin lantarki na Kaduna saboda ƙin biyan harajin N464m

An garƙame hedkwatar kamfanin lantarki na Kaduna saboda ƙin biyan harajin N464m

- Hukumar tattara haraji na jihar Kaduna ta rufe ofishin kamfanin rarraba lantarki na Kaduna

- Hukumar tara harajin ta dauki wannan matakin ne domin bashin da ta ke bi na Naira miliyan 464

- Sai dai wani jami'in kamfanin lantarkin ya ce abin da aka yi bai dace ba domin suma suna bin hukumomin jihar Kaduna kimanin N2bn amma ba su taba yanke musu wuta ba

Hukumar tara kudaden shiga na jihar Kaduna, KADIRS, ta kulle hedkwatar hukumar rarraba lantarki na jihar Kaduna (Kaduna Electric) kan kin biyan haraji da ya kai Naira miliyan 464, Daily Trust ta ruwaito.

Hukumar ta shafinta na Twitter ta ce tun daga shekarar 2012 zuwa 2018 ne aka ki biyan harajin.

An kulle hedkwatar hukumar lantarki na Kaduna saboda ƙin biyan harajin N464m
An kulle hedkwatar hukumar lantarki na Kaduna saboda ƙin biyan harajin N464m. Hoto: @daily_trust
Asali: Twitter

Sai dai mahukunta hukumar lantarkin na Kaduna ba ta ce komai ba game da batun kawo yanzu.

DUBA WANNAN: Kotun shari'a ta raba aure a Zamfara saboda tsabar girman mazakutar miji

Wakilin majiyar Legit.ng wanda ya ziyarci kamfanin ya lura cewa an rufe kofar shiga an saka alama da rubutu mai launin ja da hana shiga.

Ya kuma lura cewa ma'aikatan sun watse sai dai masu gadi kawai suke kofar shiga hedkwatan na kamfanin lantarkin.

Wani ma'aikacin kamfanin lantarkin da ya yi magana amma ya ce a sakaya sunansa ya ce, "Abin takaici ne matakin da hukumar tara harajin Kaduna ta yi kan rashin biyan harajin na N464,486,991.53k a yayin da kamfanin ke bin ma'aikatu da hukumomin gwamnatin jihar bashin da ya kai Naira Biliyan 2 na kudin lantarki da suka sha."

KU KARANTA: Ali Sarkin Mota: Allah ya yi wa direban Sardauna rasuwa

Ya ce duk da matsin lambar da hukumar samar da lantarki na kasa ke musu domin su biya kudaden, kamfanin lantarkin na Kaduna bai taba daukan matakin yanke wuta a hukumomi da ma'aikatun jihar ba.

A wani labarin daban kun ji cewa 'yan sanda a jihar Kano sun ceto wata yarinya mai shekaru 15, Aisha Jibrin, da iyayenta suka kulle ta a daki tsawon shekaru 10 a Darerewa Quaters a karamar hukumar Fagge ta jihar Kano.

Mai magana da yawun rundunar yan sandan Kano, Abdullahi Kiyawa cikin sanarwar da ya fitar a ranar Talata ya ce mahaifiyarta Rabi Muhammad tana hannunsu amma mahaifinta ya tsere.

Mai magana da yawun rundunar yan sandan Kano, Abdullahi Kiyawa cikin sanarwar da ya fitar a ranar Talata ya ce mahaifiyarta Rabi Muhammad tana hannunsu amma mahaifinta ya tsere.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel