A karon farko: Dan Najeriya ya samu shiga kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid

A karon farko: Dan Najeriya ya samu shiga kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid

- A karon farko cikin tarihin Real Madrid, babbar kungiya a kasar Spain da nahiyar turai, ta mallaki dan wasa dan asalin Najeriya

- Matashin dan wasa mai shekaru 20, Olawale Akinlabi, ya taka leda ranar Lahadi tare da Real Madrid a wasan da ta buga da kungiyar Real Sociedad a gasar Laliga

- An haifi Akinlabi a garin Mallorca na kasar Spain, amma mahaifinsa dan Najeriya ne, mahaifiyarsa kuma 'yar kasar Korea

Olawale Akinlabi, matashi dan asalin Najeriya mai shekara 20, ya cimma burinsa na fara taka leda a kungiyar kwallon kafa Real Madrid da ke kasar Spain.

Akinlabi ya taka leda a wasan da kungiyar Real Madrid ta buga da kungiyar Real Sociedad a ranar Lahadi.

An saka matashi Akinlabi a minti na 70 a wasan da aka tashi kunne doki a tsakanin Real Madrid da Real Sociedad.

Akinlabi, wanda ake kira da Marvin, zai iya taka leda a kungiyar kwallon kafa ta kasashe uku saboda asalin iyayensa.

An haifi Akinlabi a birnin Palma de Mallorca na kasar Spain amma iyayensa baki ne; mahaifinsa dan Najeriya, mahaifiya 'yar Korea.

Kafin ya samu shiga babbar kungiyar Real Madrid wacce ke karkashin kociya Zinedine Zidane, Akinlabi ya na taka leda a karamar kungiyar Real Madrid.

DUBA WANNAN: Liverpool ta sayi gogagen dan wasan tsakiya daga Bayern Munich

Kafin zuwansa karamar kungiyar Real Madrid a shekarar 2016, Akinlabi ya samu horo a makarantun kungiyoyin kwallon kafa na kasar Spain da yawa.

Duk da wasu rahotanni sun nuna cewa hukumar kungiyar kwallon kafa ta kasa sun tuntubi Akinlabi, ya zabi ya taka leda da kungiyar kasar Spain.

A karon farko: Dan Najeriya ya samu shiga kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid
Akinlabi
Source: Twitter

Tuni Akinlabi ya fara bugawa kasar Spain wasanni a karamar kungiyarta a gasar kasashen nahiyar Turai.

A cikin watan Yuli ne kungiyar Real Madrid ta sake lashe kofin gasar kwallon kafa ta kasar Andolus, wacce aka fi sani da 'Spain', a karo na 34.

DUBA WANNAN: Nigeria ta samu babban ci gaba a kwallon duniya, ita ce ta 29 - FIFA

Real Madrida ta samu nasarar kwace kofin Laliga daga hannun babbar abokiyar hamayyarta, kungiyar Barcelona wacce ke rike da kofin a kakannin wasa biyu da suka gabata.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel