Dubunnan yan Najeriya sun gudu jamhuriyyar Nijar bayan harin Boko Haram

Dubunnan yan Najeriya sun gudu jamhuriyyar Nijar bayan harin Boko Haram

- An yi musayar wuta tsakanin Sojoji da yan ta'addan ISWAP a Damasak

- Wannan ya biyo bayan harin da suka kai gari ranar Talata

- Mutanen garin sun fara guduwa zuwa garin Diffa a nijar

Yan Najeriya kimanin 100,000 dake garin Damasak sun arce jamhurriyar Nijar, yayinda Boko Haram suka kai hari hedkwatar karamar hukumar karo biyar cikin makonni biyu.

Bidiyo daga HumAngle ya nuna yadda wasu ke gudu da kayayyakin kan jakuna a Damasak.

Wakilin HumAngle, Murtala, ya bayyana cewa mutanen sun gudu ne sakamakon hare-haren duk da yukurin da akayi wajen fada musu su zauna.

Hakazalika kungiyiyin tallafa sun gudu daga yankin sakamakon hare-haren Boko Haram ba kakkautawa, yace.

Jawabin yace: "Yan Najeriya a Damasak sun guduwa Diffa, jamhurriyar Nijar ta rafin Kamadougou da ya raba yankunan biyu."

DUBA NAN: Yan bindiga kai farmaki kwalejin Soji dake Kaduna

KU KARANTA: Gwamnan Edo karya yake, bamu buga N60bn don rabawa gwamnoni ba: Gwamnatin Tarayya

Bayan harin jiya, da safiyar yau anyi artabu tsakanin yan ta'addan da sojoji a Damasak.

Sojojin sun fatattaki masu tayar da kayar bayan daga garin amma sai suka dawo da safiyar ranar Laraba, suna harbi ba kakkautawa sannan suna cinnawa gidaje wuta.

A cewar wata majiyar sojoji, maharan na matukar neman karbe ikon garin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel