Yanzu Yanzu: Ana musayar wuta tsakanin Boko Haram da sojoji a Borno

Yanzu Yanzu: Ana musayar wuta tsakanin Boko Haram da sojoji a Borno

- Ana musayar wuta tsakanin mayaƙan da ake zargi Boko Haram ne da sojoji a garin Damasak na jihar Borno

- Wata majiya daga sojoji ta ce mayaƙan sun ɗage akan sai sun ƙwace garin Damasak

- Wani jami'in tsaron sa kai na Civilian JTF ya tabbatar da cewa an shafe tsawon sa'a uku ana bata-kashi da mayakan

A yanzu haka, wasu da ake zargin ‘yan kungiyar Boko Haram ne suna cikin artabu da sojoji a Damasak da ke jihar Borno.

Sojojin sun fatattaki masu tayar da kayar bayan daga garin amma sai suka dawo da safiyar ranar Laraba, suna harbi ba kakkautawa sannan suna cinnawa gidaje wuta.

KU KARANTA KUMA: Yanzu-yanzu: Tsohon gwamnan Oyo da Ondo a mulkin soja, Usman, ya mutu

Yanzu Yanzu: Ana musayar wuta tsakanin Boko Haram da sojoji a Borno
Yanzu Yanzu: Ana musayar wuta tsakanin Boko Haram da sojoji a Borno Hoto: brickswrites.com.ng
Asali: UGC

A cewar wata majiyar sojoji, maharan na matukar neman karbe ikon garin, jaridar Daily Trust ta ruwaito.

“Zan iya tabbatar da cewa sojoji ke da iko da garin Damasak amma ana ci gaba da fafatawa. Kun san tsawon wani lokaci yanzu, yan ta’addan sun addabi garin Damasak amma ba za su iya yin nasara ba saboda sojojin mu na nan a kasa,” in ji majiyar.

Haka kuma wata majiya ta JTF ta tabbatar da cewa an kwashe kusan awanni uku garin na karkashin hari.

"Akwai bukatar dukanmu mu yi addu'a domin sojojinmu su yi nasara a kan wadannan mugayen mutane, Boko Haram sun koma Damasak bayan harin Asabar, kawai mu yi wa sojojin addu'a," in ji shi.

KU KARANTA KUMA: Tashin hankali: An gano gawawwaki ba tare da kai ba a karkashin gada a Cross River

Wasu yan ta’adda sun kai hari a Damasak a karshen makon da ya gabata kuma akalla mutane shida aka kashe yayin da aka kona wasu gine-ginen jama'a.

A wani labarin, yayin ganawar da Fasto Enoch Adeboye yayi da Nasir El-Rufai a ranar Talata 13 ga Afrilu, ya bayyana wasu bayanan sirri game da gwamnan na Kaduna.

Ziyarar Adeboye zuwa gidan gwamnatin jihar ta zo ne a daidai lokacin da aka sako mambobin cocin Redeemed Christian Church of God (RCCG), jaridar Punch ta ruwaito.

A cewar jaridar Daily Trust, a ziyarar, shahararren malamin ya bayyana cewa ya dade da sanin gwamnan, ya kara da cewa gwamnan ya kasance mutum mai kirki.

Asali: Legit.ng

Online view pixel