Gwamnan Edo karya yake, bamu buga N60bn don rabawa gwamnoni ba: Gwamnatin Tarayya
- Gwamna Obaseki na jihar Edo ya fasa kwai kan kudin da aka raba musu a Maris
- Ministar Kudi, Zainab Shamsuna tace karya ne, babu gaskiya cikin jawabinda
- Shin wa za'a gaskata kuma wa za'a karyata?
Gwamnatin tarayya ta siffanta kalaman gwamnan jihar Edo, Godwin Obaseki, na cewa an buga kudi N60bn don rabawa gwamnoni a matsayin karya marasa tushe da asali.
Ministar kudi da kasafi, Zainab Ahmed Shamsuna, ta bayyana hakan yayin hira da manema labaran fadar shugaban kasa ranar Laraba, rahoton TheCable.
"Maganar da gwamnan Edo yayi gaskiya ya yi matukar bata min rai. Saboda ba gaskiya bane," Zainab tace.
"Kudin da muke rabawa na FAAC kudi ne da aka samu kuma kowa ya nada labari. Muna wallafa kudin da FIRS, Kwastam da NNPC suka samo kuma mu raba. Saboda haka ba gaskiya bane cewa mun buga kudi don rabo, karya ne."
KU DUBA: Ganduje ya gina wa Almajirai makarantun tsangaya uku a jihar Kano
KU KARANTA: Gwamnan Yobe an angwance da diyar marigaryi Abacha, Hajiya Gumsu
Mun kawo muku cewa Gwamnan jihar Edo, Godwin Obaseki, ya bayyana cewa Najeriya na cikin halin rashin kudi saboda sai da aka buga wasu biliyoyi a watan Maris aka rabawa jihohi.
Gwamnan ya ce kudin wata-wata da ake rabawa gwamnoni bai kai ba, sai da gwamnatin tarayya ta buga sabbin kudi bilyan 50 zuwa 60 aka raba musu.
"Lokacin da aka biyamu kudin wata-wata na Maris, sai da gwamnatin tarayya ta buga N50-N60 billion don kudin su isa a raba mana," Obaseki ya bayyana ranar Alhamis.
Asali: Legit.ng