Da duminsa: Yan bindiga kai farmaki kwalejin Soji dake Kaduna

Da duminsa: Yan bindiga kai farmaki kwalejin Soji dake Kaduna

- Yan bindiga sun shiga garkuwa da mutane a barikin Sojoji

- Wannan ya biyo bayan sace daliban makarantar FCFM dake Afaka

Wasu yan bindiga yanzu haka sun kai farmaki kwalejin Sojoji dake gari Jaji, karamar hukumar Igabi ta jihar Kaduna.

A cewar Daily Trust, wasu mazauna garin sun bayyana cewa yan bindigan sun je garkuwa da wasu ma'aikatan kwalejin ne da kuma mazauna garin.

Kwalejin horon Sojin Jaji shahrarren makaranta ne da ake horon Sojojin kasa, na sama da kuma na ruwa.

Wani mazauni gairn mai suna Adamu, ya bayyanawa Daily Trust cewa yan bindigan sun dade suna addaban mazauna kwalejn da kauyukan dake makwabtaka da kwalejin.

"Allah kadai ke karemu. Sun dade suna kwace masa shanu. Sojoji na bude musu wuta shi yasa basu samun kashe mutane," Adamu yace.

DUBA NAN: Gwamnan Edo karya yake, bamu buga N60bn don rabawa gwamnoni ba: Gwamnatin Tarayya

Da duminsa: Yan bindiga kai farmaki kwalejin Soji dake Kaduna
Da duminsa: Yan bindiga kai farmaki kwalejin Soji dake Kaduna
Asali: Original

KU KARANTA: Gwamnan Yobe an angwance da diyar marigaryi Abacha, Hajiya Gumsu

Kwamandan kwalejin, Air Marshal Olayinka Alade, ya tabbatar da hakan ranar Laraba a Abuja yayinda ya kai ziyara hedkwatar Soji domin ganawa da shugaban hafsan Soji, Laftanan Janar Attahiru Ibrahim.

Kwamandan ya ce a ranar Talata, 13 ga watan Afrilu, yan bindiga sun kora wasu shanu a bayan kwalejin bayan musayar wuta da Sojoji.

Yace: "Ko jiya (Talata), na samu labarin wasu yan bindiga sun kora shanu a bayanmu. Wasu hafsoshinmu na atisaye a wajen. Sun yi arangama da yan bindigan kuma sai da sukayi musayar wuta a lokacin."

A bangare guda, Gwamnan jihar Ebonyi, Dave Umahi, ya bayyana cewa wasu mutane na kokarin jefa yankin Kudu maso gabas (yankin Igbo) cikin yaki.

Magana yayin hira da ChannelsTV, Umahi ya ce wasu yan bindiga ke tayar da tarzoma suna kashe mutane da sunan yan kungiyar IPOB.

Duk da cewa bai ambaci sunayen wadanda yake zargi ba, ya yi gargadin cewa gwamnonin yankin ba zasu zuba ido a jefasu cikin rudani ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng