Jack Dorsey Ya Sayar Da Rubutun Da Aka Fara Wallafawa a Twitter Kan Kudi $2.9m

Jack Dorsey Ya Sayar Da Rubutun Da Aka Fara Wallafawa a Twitter Kan Kudi $2.9m

- Mai kamfanin Twitter, Jack Dorsey ya sayar da rubutun farko da ya fara wallafawa a manhajar

- Dorsey ya sayar da rubutun ga wani dan kasar Malaysia mai suna Sina Estavi kan kudi Dalla miliyan 2.9

- Bayan kammala cinikin, Dorsey ya sadaukar da dukkan kudin domin tallafawa mutanen nahiyar Afirka don rage radadin korona

Jack Dorsey, Mai Kamfanin Twitter ya sayar da sakon da aka fara wallafawa a manhajar ga wani dan kasar Malaysia mai suna Sina Estavi.

A wani sako da ya wallafa a ranar Litinin, Dorsey ya ambaci sunan wanda ya siya rubutun ya kuma bayyana kudin da ya saya.

DUBA WANNAN: Mutum 19 Sun Rasu, 34 Sun Jikkata Sakamakon Hatsarin Mota a Hanyar Kaduna Zuwa Abuja

An Sayar Da Rubutun Farko a Twitter Kan Kudi Dalla Biliyan 2.9
An Sayar Da Rubutun Farko a Twitter Kan Kudi Dalla Biliyan 2.9. Hoto: @jack
Source: Twitter

A ranar 21 da ga watan Maris na 2006 ne Dorsey ya wallafa sakon na farko a Twitter "just setting up my twttr".

An yi ciniki sannan aka biya kudin da kudin intanet na NFT da ya yi fice a shekarar 2021.

NFT na amfani da fasahar blockchain ne kamar irin su Bitcoin wadda dukkan masu amfani da shi za su iya tabbatar da cinikayyar da aka yi.

Dorsey ya sayar da NFT dinsa a wani manhaja da ake kira Valuables mallakar wani kamfanin Amurka mai suna Cent.

DUBA WANNAN: Da Ɗumi-Ɗumi: Jam'iyyar APC Ta Bawa Ambode Sabon Muƙami

Cameron Hejazi, shugaban Cent ya tabbatar da cinikin inda ya ce an siya NFT da kudin crypto na Ether kan 1630.5825601 ETH. Darajarsa a lokacin da aka siyar ya kai $2,915,835.47.

Kazalika, Shugaban na Twitter ya ce ya sadaukar da kudin da ya siyar da sakon farkon ga kungiyoyin taimakawa mutane a Afirka da annobar korona ta yi wa illa.

Da ya ke magana kan rubutun da ya siya, Estavi ya ce 'wannan ba rubutu bane kamar saura, Ina ganin nan da wasu shekaru mutane za su gane darajarsa kamar zanen Mona Lisa.'

Aminu Ibrahim ɗan jarida ne kuma ɗalibi mai neman ilimi. Ya yi karatun digiri na farko a Jami'ar Ahmadu Bello Zaria, yanzu yana karatun digiri na biyu a Jami'ar Gwamnatin Tarayya da ke Dutse, Jihar Jigawa.

Ya shafe kimanin shekaru 5 yana aikin jarida inda ya samu gogewa a ɓangaren rubutun Hausa akan fanoni da suka shafi siyasa, mulki, wasanni, nishadi, da sauransu. Aminu Ibrahim ne ya samu lambar yabo na zakaran editan shekarar 2020.

Za'a iya bibiyarsa a shafinsa na Twitter @ameeynu

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel