Mutum 19 Sun Rasu, 34 Sun Jikkata Sakamakon Hatsarin Mota a Hanyar Kaduna Zuwa Abuja

Mutum 19 Sun Rasu, 34 Sun Jikkata Sakamakon Hatsarin Mota a Hanyar Kaduna Zuwa Abuja

- Mutane 19 sun rasu sakamakon hatsarin mota a hanyar Kaduna zuwa Abuja

- Wasu mutanen 34 sun samu raunuka sakamakon hatsarin da ya faru a Kateri

- Kwamishinan tsaro na jihar Kaduna, Samuel Aruwan ya tabbatar da fakuwar hatsarin

A kalla mutane goma sha tara sun riga mu gidan gaskiya sakamakon hatsarin mota da ya afku a babban titin Kaduna zuwa Abuja.

Hatsarin ya faru ne a ranar Lahadi a kusa da Kateri a babban titin Kaduna zuwa Abuja a cewar sanarwar da kwamishinan tsaro na jihar Kaduna, Samuel Aruwan ya sanar a shafinsa na Facebook.

Rayyuka 19 Sun Salwanta, 34 Sun Jikkata Sakamakon Hatsarin Mota a Hanyar Kaduna zuwa Abuja
Rayyuka 19 Sun Salwanta, 34 Sun Jikkata Sakamakon Hatsarin Mota a Hanyar Kaduna zuwa Abuja. Hoto: Samuel Aruwan
Asali: Facebook

DUBA WANNAN: Matar Da Za Ta Auri Sojan Saman Da Aka Kashe a Kaduna Ta Auri Yayansa

Kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida, Samuel Aruwan ya yi bayanin cewa hatsarin ya faru ne a yammacin ranar Lahadi da ya ritsa da DAF sakamakon gudu fiye da kima.

Ya yi bayanin cewa tayar motar ta fashe hakan yasa motar ta kwace wa direba sannan ta fada cikin daji.

Mr Aruwan ya ce a kalla mutane 53 ne hatsarin ya ritsa da su; 16 sun mutu nan take sannan wasu uku suka mutu daga baya.

Wasu mutane talatin da hudu sun jikkata, jami'an hukumar kiyayye haddura na kasa, FRSC, sun garzaya da su asibiti domin a yi musu magani.

KU KARANTA: Yanzu-Yanzu: An Kai Hari Gidan Mahaifiyar Sunday Igboho

A cewar wasu da abin ya faru a idonsu, mafi yawancin fasinjojin da ke cikin motar an dakko su ne daga Kara, kusa da gidan man fetur, inda wasu za a sauke su a Zaria, yayin da sauran za su sauka a Kano.

Gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai ya nuna bakin cikinsa kan hatsatrin inda ya yi addu'ar Allah ya jikan wadanda suka rasu yayin da ya aike da sakon ta'aziyya ga iyalansu.

Ya kuma yi wa wadanda suka jikkata fatan samun sauki cikin gaggawa.

Gwamnan ya kuma shawarci direbobi su rika takatsantsan a dukkan lokuta tare da kauracewa gudu fiye da ka'ida da sauran ganganci a titi.

A wani rahoton, kun ji Rundunar yan sandan jihar Sokoto, a ranar Alhamis, ta ce ta kama a kalla mutane 17 kan zargin fashi da makami, garkuwa da mutane da wasu laifuka a jihar.

Mr Kamaldeen Okunlola, kwamishinan yan sandan jihar ne ya sanarwar manema labarai hakan a Sokoto, Vanguard ta ruwaito.

Okunlola ya ce rundunar a ranar 4 ga watan Maris ta kama wani Jabbi Wanto kan hadin baki da sace mutane biyu a Tamba Garka a karamar hukumar Wurno na jihar.

Aminu Ibrahim ɗan jarida ne kuma ɗalibi mai neman ilimi. Ya yi karatun digiri na farko a Jami'ar Ahmadu Bello Zaria, yanzu yana karatun digiri na biyu a Jami'ar Gwamnatin Tarayya da ke Dutse, Jihar Jigawa.

Ya shafe kimanin shekaru 5 yana aikin jarida inda ya samu gogewa a ɓangaren rubutun Hausa akan fanoni da suka shafi siyasa, mulki, wasanni, nishadi, da sauransu.

Aminu Ibrahim ne ya samu lambar yabo na zakaran editan shekarar 2020.

Za'a iya bibiyarsa a shafinsa na Twitter a @ameeynu

Asali: Legit.ng

Online view pixel