COVID-19: Kungiyar Likitoci ta na barazanar shiga yajin-aiki 'saboda rashin biyan hakkoki'

COVID-19: Kungiyar Likitoci ta na barazanar shiga yajin-aiki 'saboda rashin biyan hakkoki'

- Gwamnati ta yi alkawarin biyan iyalan Likitocin da cutar COVID-19 ta kashe

- Coronavirus ta kashe Likitoci a Najeriya amma ba a ba magadansu komai ba

- NARD ta ce za su tafi yajin-aiki bayan wasu sun yi watanni uku babu albashi

Kungiyar manyan likitocin Najeriya watau NARD, ta ce gwamnatin tarayya ta yi watsi da iyalan likitocin da su ka mutu a wajen kula da masu cutar COVID-19.

Shugaban kungiyar NARD na kasa, Dr. Uyilawa Okhuaihesuyi ya yi hira jaridar Punch a ranar Alhamis, 18 ga watan Maris, 2021, inda ya bayyana korafinsu.

Duk da gwamnati ta ware Naira biliyan 500 domin yaki da annobar COVID-19 a 2020, ba a biyan iyalan likitocin da su ka mutu a sanadiyyar cutar hakkokinsu.

Shugaban kwamitin PTF kuma sakataren gwamnatin Najeriya, Boss Mustapha ya yi a alkawarin za a rika biyan iyalan likitocin da su ka mutu kudin hakkin rai.

KU KARANTA: NDLEA ta yi ram da kwayoyin N60bn a kwanaki 60 - Marwa

Shugaban wannan kungiya yake cewa daga bara zuwa yanzu, COVID-19 ta kashe likitoci 17, amma gwamnati ba ta ba magadansu kudin da ta yi alkawari ba.

Uyilawa Okhuaihesuyi ya ce kwararrun likitocin kasar nan za su tafi yajin-aiki a ranar 31 ga watan Maris.

“Likitocin da ke karkashin manhajar GIMFIS sun shafe watanni ba tare da an biya su albashi ba, kuma ana so a hana likitoci ficewa daga kasar nan?" Inji NARD.

“Kusan likitocinmu 3, 824 su ka gamu da barazanar COVID-19, yayin da 1, 600 su ka kamu. Kimanin 17 su ka mutu. Gwamnati sun yi alkawarin biyan inshora.”

KU KARANTA: ‘Yan uwan Faston da aka sace a Neja sun ce ba su da kudin fansa

COVID-19: Kungiyar Likitoci ta na barazanar shiga yajin-aiki 'saboda rashin biyan hakkoki'
Takardar NARD Hoto: @nard_nigeria
Source: Twitter

Okhuaihesuyi ya ce: “Da na ke magana yanzu. Babu abin da aka yi. Babu iyalin wanda aka biya, duk da su na ikirarin an ba likitoci inshora. Yaudarar fatar baki ce.”

“Wanda na gada a ofis ya gana da Ministoci irinsu Festus Keyamo, Olorunnimbe Mamora, Osagie Ehanire da Chris Ngige.” Likitan ya ce duk da haka har yanzu shiru.

A makon nan ne shugaban hukumar NPHCDA, Dr. Faisal Shuaib ya ce kowace Jiha ta karbi maganin cutar Coronavirus illa Jihar Kogi, saboda wasu dalilai.

NPHCDA ta yi bayanin abin da ya hana Gwamnatin Kogi karbar rigakafin ba AstraZeneca.

Faisal Shuaib ya ce a Kogi akwai rashin dakuna masu sanyi da za a adana maganin. Shuaib yake cewa gwamnatin jihar ba ta yi tanadin wurin ajiyen maganin ba.

M. Malumfashi ma'aikacin jaridar Legit.ng ne wanda ya shafe kusan shekaru 5 ya na wannan aiki. Ya yi Digirin farko a ilmin komfuta da Digirgir a harkar bayanai, kuma ya na Digirgir a ilmin aikin jarida.

Malumfashi ya kan buga labarai, ya yi rubuce-rubuce a harkar siyasa, wasanni da addini. Ya yi rubuce-rubuce barkatai a gidajen jaridun Najeriya.

A bibiye shi a Twitter @m_malumfashi

Source: Legit.ng

Online view pixel