‘Yan bindiga sun dura Kauye a Tegina, sun sace Fasto, sun ce sai an biya Naira Miliyan 60

‘Yan bindiga sun dura Kauye a Tegina, sun sace Fasto, sun ce sai an biya Naira Miliyan 60

- Dazu nan aka shiga har gida aka yi ram da wani Fasto a Unguwar Saye

- Wadanda su ka sace Faston sun ce sai an biya N60m kafin su fito da shi

- ‘Yan bindiga sun addabi kauyen Tegini da ke cikin karamar Rafi, a Neja

Jaridar The Nation ta fitar da rahoto cewa ‘yan bindiga sun sace wani fasto a wani kauye a karamar hukumar Rafi, jihar Neja a ranar Alhamis.

Wannan fasto mai suna Yohanna Gyang Bitrus da aka dauke shi ne ke kula da cocin Shiyona Baptist da ke Unguwar Saye a kauyen Yakila a Tegina.

Kamar yadda rahotonni su ka bayyana, an dauke faston ne da kusan karfe 2:00 na rana a dazu.

‘Yan bindigan sun shigo Unguwar Saye da ke kauyen na Yakila ne da rana tsaka, ba su zarce ko ina ba sai gidan wannan faston, su ka yi gaba da shi.

KU KARANTA: An shigo kauye an kashe Mai kudi, an sace dukiya, an tafi da yaransa

Wadannan ‘yan bindiga sun yi ta harbe-harbe a iska da nufin tsorata sauran mutanen kauyen, amma ba su yi yunkurin shiga wani gida ko taba wasu ba.

Jim kadan bayan an dauke malamin addinin na kirista, ‘yan bindigan su ka tuntubi ‘yanuwansa su ka tabbatar da cewa sai an biya kudi kafin su sake shi.

Makusantan faston sun ce ‘yan bindigan sun bukaci su biya Naira miliyan 60 a matsayin kudin fansa.

Wani daga cikin ‘yan uwan malamin kiristan ya shaida wa manema labarai cewa ba su san inda za su shiga, su tattaro wannan makudan miliyoyin kudi ba.

KU KARANTA: 'Yan bindiga sun auka makarantar firamare a Kaduna

‘Yan bindiga sun dura Kauye a Tegina, sun sace Fasto, sun ce sai an biya Naira Miliyan 60
Gwamna Abubakar Sani Bello Hoto: @Abusbello
Asali: Twitter

Da aka tuntubi jami’an tsaro sun ce ba su kai ga samun labarin abin da ya faru ba. Kakakin ‘yan sandan Neja, DSP Wasiu Abiodun ya ce za su binciki lamarin.

A cikin makon nan ne aka ji cewa an samu wasu 'yan bindiga sun budewa tawagar motocin Sarkin Birnin Gwari, Alhaji Zubairu Jibril Mai Gwari II, wuta.

Rahotanni sun ce an kai wa motocin Sarkin na Birnin Gwari hari ne a hanyar Kaduna zuwa Birnin-Gwari da yammacin ranar Talata, 17 ga watan Maris, 2021.

Direban Mai martaba, Umar Jibril, ya bayyana cewa Sarkin ya na wani wuri a lokacin da aka kai harin.

M. Malumfashi ma'aikacin jaridar Legit.ng ne wanda ya shafe kusan shekaru 5 ya na wannan aiki. Ya yi Digirin farko a ilmin komfuta da Digirgir a harkar bayanai, kuma ya na Digirgir a ilmin aikin jarida.

Malumfashi ya kan buga labarai, ya yi rubuce-rubuce a harkar siyasa, wasanni da addini. Ya yi rubuce-rubuce barkatai a gidajen jaridun Najeriya.

A bibiye shi a Twitter @m_malumfashi

Asali: Legit.ng

Online view pixel