Da dumi-dumi: Kungiyar Kirista ta Nigeria ta maka gwamnatin tarayya a kotu saboda CAMA

Da dumi-dumi: Kungiyar Kirista ta Nigeria ta maka gwamnatin tarayya a kotu saboda CAMA

- Kungiyar Kirista ta Nigeria, CAN ta yi karar gwamnatin tarayya a wani kotu da ke Abuja

- Kungiyar CAN ta shigar da karar ne domin nuna kin amincewarta da wasu sassa na dokar CAMA 2020 da gwamnati ta amince da shi

- Dokar dai ya bawa gwamnati dama sa ido kan yadda kungiyoyi da kamfanoni ke kashe kudadensu ciki har da coci

- Kungiyar ta CAN na ganin damar da dokar ta bawa gwamnati tamkar katsalandan ne ga harkokin addinin kirista ta coci-coci

Kungiyar Kirista ta Nigeria, CAN, ta maka gwamnatin tarayyar kasa a kotu tana kallubalantar wasu sassan dokar maida kamfanoni da kungiyoyi karkashin sa-idon gwamnati ta 'Companies and Allied Matters Act 2020' da aka fi sani da CAMA, The Punch ta ruwaito.

A cikin sanarwar da sakataren kungiyar, Joseph Daramola ya fitar a ranar Litinin, ya ce kungiyar ta Kirista bata gamsu da wasu sassa na dokar ta CAMA 2020 ba don haka ta yanke hukuncin kallubalantar dokar a kotu.

Da dumi-dumi: Kungiyar Kirista ta Nigeria ta maka gwamnatin tarayya a kotu saboda CAMA
Da dumi-dumi: Kungiyar Kirista ta Nigeria ta maka gwamnatin tarayya a kotu saboda CAMA. Hoto: @MobilePunch
Source: Twitter

An shigar da karar mai lamba FHC/ABJ/CS/244/2021 a babban kotun Abuja tsakanin kungiyar ta CAN da Hukumar yi wa kamfanoni rajista tare da Ministan Masana'antu, Cinikayya da Saka Hannun Jari a cewar sanarwar.

"Kungiyar ta yanke shawarar zuwa kotu ne bayan dukkan kokarin da ta yi na gamsar da gwamnatin ta sauya wasu sassan dokar na hana gwamnati yin katsalandan a harkokin coci bai yi wu ba," a cewar wani bangare na sanarwar.

Tun a watan Agustan 2020 ne Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya rattaba hannu kan dokar ta CAMA 2020, Majalisar tarayya ita ma ta amince da dokar inda ta maye gurbinta da 1990 CAMA.

Amma manyan fastoci kamar su David Oyedepo na Living Faith Church Worldwide da wasu fastocin sun nuna kin amincewarsu da dokar.

A wani rahoton daban kun ji cewa, rundunar yan sandan jihar Kano ta kwantar da jama'a hankula game da wasu bakin mutane tare da rakuma da suka bayyana a wasu sassan jihar.

Daily Nigerian ta gano cewa mazauna jihar sun ankarar da yan sanda kan bakin mutanen da suka yada zango a wasu sassan jihar.

Wasu mazauna garin suna zargin matafiyar sun iso jihar ne domin aikata laifi da sunan fataucin kanwa.

Aminu Ibrahim ɗan jarida ne kuma ɗalibi mai neman ilimi. Ya yi karatun digiri na farko a Jami'ar Ahmadu Bello Zaria, yanzu yana karatun digiri na biyu a Jami'ar Gwamnatin Tarayya da ke Dutse, Jihar Jigawa.

Ya shafe kimanin shekaru 5 yana aikin jarida inda ya samu gogewa a ɓangaren rubutun Hausa akan fanoni da suka shafi siyasa, mulki, wasanni, nishadi, da sauransu.

Aminu Ibrahim ne ya samu lambar yabo na zakaran editan shekarar 2020.

Za'a iya bibiyarsa a shafinsa na Twitter a @ameeynu

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel