Yanzu-yanzu: 'Yan fashi da makami sun kai hari banki a Osun, sun kashe mutum 5

Yanzu-yanzu: 'Yan fashi da makami sun kai hari banki a Osun, sun kashe mutum 5

- Gungun yan fashi da makami sun kai hari wani bankin zamani a jihar Osun

- Lamarin ya faru ne a ranar Alhamis 11 ga watan Maris na shekarar 2021 a garin Okuku

- Yemisi Opalola, Mai magana da yawun yan sandan jihar ta tabbatar da afkuwar lamarin

Hankulan mutanen gari ta tashi a garin Okuku da Odo-Otin a jihar Osun a yayin da ƴan fashi da makami da ba a san adadinsu ba suka yi kutse a wani bankin zamani.

The Nation ta ruwaito cewa ƴan bindigan sun afka bankin da misalin ƙarfe 12 na rana suna harbe-harbe don firgita mutane kafin su aikata mummunan nufin su.

Yanzu-yanzu: Yan fashi da makami sun kai hari banki a Osun
Yanzu-yanzu: Yan fashi da makami sun kai hari banki a Osun. Hoto: @thecableng
Source: Twitter

Mai magana da yawun rundunar ƴan sandan jihar Osun Mrs Yemisi Opalola ta tabbatar da afkuwar lamarin.

Ta ce, "Kwamishinan yan sandan jihar, Mr Olawale Olokode ya jagoranci tawagar yan sanda zuwa wurin da abin ya faru da nufin fatattakar yan fashin da kama su."

Nigerian Tribune ta ruwaito cewa a kalla mutane biyar sun rasu yayin da ba a tabbatar da adadin wadanda suka jikkata ba sakamakon harin.

Rahoton ya ce wani ganau ya shaidawa wakilin majiyar Legit.ng cewa yan fashin sun afka bankin misalin karfe 1 na rana suka lalata ATM din da ke gaban bankin.

An gano cewa daya daga cikin wadanda suka rasu dan acaba ne da ke tsaye a gaban bankin a yayin da yan fashin suka harbe shi.

A wani rahoton daban kun ji cewa, rundunar yan sandan jihar Kano ta kwantar da jama'a hankula game da wasu bakin mutane tare da rakuma da suka bayyana a wasu sassan jihar.

Daily Nigerian ta gano cewa mazauna jihar sun ankarar da yan sanda kan bakin mutanen da suka yada zango a wasu sassan jihar.

Wasu mazauna garin suna zargin matafiyar sun iso jihar ne domin aikata laifi da sunan fataucin kanwa.

Aminu Ibrahim ɗan jarida ne kuma ɗalibi mai neman ilimi. Ya yi karatun digiri na farko a Jami'ar Ahmadu Bello Zaria, yanzu yana karatun digiri na biyu a Jami'ar Gwamnatin Tarayya da ke Dutse, Jihar Jigawa.

Ya shafe kimanin shekaru 5 yana aikin jarida inda ya samu gogewa a ɓangaren rubutun Hausa akan fanoni da suka shafi siyasa, mulki, wasanni, nishadi, da sauransu.

Aminu Ibrahim ne ya samu lambar yabo na zakaran editan shekarar 2020.

Za'a iya bibiyarsa a shafinsa na Twitter a @ameeynu

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel