Sulhu da yan bindiga ba gajiyawa bane, Gwamnan Zamfara ya bayyana

Sulhu da yan bindiga ba gajiyawa bane, Gwamnan Zamfara ya bayyana

- Gwamna Matawalle ya karbi sabbin tubabbun yan bindigan da suka addabi jihar

- Daya daga cikinsu ya bayyana cewa ya shiga harkar tsageranci ne saboda an kashe masa iyali

- A cewar Matawalle, babu kasar da ta cigaba da duniya ba tare da sulhu ba

Gwamnan jihar Zamfara, Bello Matawalle, a ranar Litinin ta bayyana cewa sulhu da yan bindiga ba alamun gajiyawa bane.

Gwamnan ya bayyana hakan a gidan gwamnatin jihar dake Gusau yayin tarban wasu tubabbun yan bindiga da suka mika wuya tare da ajiye makamansu, Channels TV ta ruwaito.

A cewar Matawalle, sulhu da yan bindiga ne hanya daya tilo na magance matsalar tsaro a jihar.

Ya yi Alla-wadai da tunanin da wasu yan siyasa ke yi na ganin cewa sulhu da yan bindiga gajiyawa ne.

Ya ce duk wani yaki a duniya da sulhu ake kara shi.

"Ba gajiyawa bane ko abun kunya ga wani ya kadamar da sulhu. Babu inda ake smaun cigaba a duniya ba tare da sulhu ba," Matawalle yace.

"A yau kadai, makaman da ke nan na nuna irin nasarorin da muke samu saboda barin ire-iren wadannan makaman cikin daji na iya haifar da matsaloli da yawa."

"Ta hanyar kawosu wajen jami'an tsaro, mun rage musu karfi. Bari suna rike wadannan makaman cikin al'umma ne ya jefa mu cikin wannan halin," ya kara.

KU KARANTA: Direbobin keke napep sun dage yajin aiki a jihar Kano

Sulhu da yan bindiga ba gajiyawa bane, Gwamnan Zamfara ya bayyana
Sulhu da yan bindiga ba gajiyawa bane, Gwamnan Zamfara ya bayyana
Source: Facebook

KU KARANTA: El-Rufai: Najeriya ta fi kowace kasa a duniya yawan talakawa

A wani labarin kuwa, direbobin keke napep dake yajin aiki a Kano sun dakatar da matakin kuma za su ci gaba da aiki ba tare da bata lokaci ba.

Shuwagabanin hadin kan kungiyoyin masu keke napep na Najeriya sun umarci membobinsu da su ci gaba da aiki nan take.

Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin uku yanzu tare da shararriyar jarida Legit.

Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss.

Source: Legit.ng

Online view pixel