An kashe wani shahararren makashi yayin musayar wuta a Ogun

An kashe wani shahararren makashi yayin musayar wuta a Ogun

- Yan sanda sun harbi wani mutum da rundunar ke nema ruwa a jallo a Jihar Ogun

- Mutumin da ake zargin dan kungiyar asiri kuma makashi ne ya gamu da ajali bayan da yan sanda suka harbe shi

- Ya rasu yayin da yake karbar magani a gadon asibiti, sai dai hukumar ta ce ya amsa laifukan sa kafin ya mutu

An ruwaito cewa yan sanda sun harbe wani dan kungiyar asiri kuma makashi, Owolabi Oludipe da aka fi sani da Somori a Jihar Ogun, The Punch ta ruwaito.

An harbe wanda ake zargin a musayar wuta da yan sanda ranar Lahadi, 31 ga Janairu a yankin Odogbolu da ke jihar kamar yadda rahotanni suka bayyana.

Mai magana da yawun rundunar yan sanda, DSP Abimbola Oyeyemi wanda ya tabbatar da faruwar lamarin ga yan jarida ranar Litinin a Abeokuta, ya ce wanda ake zargin sunan sa ya dade cikin jerin wanda hukumar ke nema ruwa a jallo tsawon lokaci.

An kashe wani shahararren makashi a musayar wuta a Ogun
An kashe wani shahararren makashi a musayar wuta a Ogun. Hoto: Channels TV
Source: Twitter

Sunan wanda ake zargin ya shiga jerin ne biyo bayan zargin sa da kashe wani jami'in Civil Defence, Rusewe Segun a Nuwambar da ta gabata.

An kuma ruwaito cewa ya kashe wani Sunday Kayode Adegbuiyi a Fabarairu, 2020.

Wanda ake zargin har ila yau, shi ya kashe shugaban kungiyar asiri ta Eiye, Shoyombo Sanyaolu Fakayo a Nuwamba, 2020 lokacin rikicin wacce kungiya ce babba tsakanin biyun.

A cewar Oyeyemi, an hangi wanda ake zargin a Ita-Ado da ke Odogbolu inda shi da sauran yan kungiyar asiri ta Aiye su ke shirya sake kai hari kan mutanen yankin.

Yan sanda, da suke kokarin damke tawagar, da suka ga yan sandan, sai suka fara harbin su, yayin mayar da martani aka harbi shugaban su "Somori" kuma yaji rauni, yayin da wasu suka gudu cikin daji dauke da makaman su.

"An garzaya da shi asibiti cikin gaggawa, sai dai ya mutu lokacin da ya ke karbar magani.

"Ya amsa duk kashe kashen a gadon asibiti kafin ya mutu. An samu wasu tarin layoyin asiri da ya sanya a gaba daya jikin sa, harsashi guda biyu da kuma wayar hannu," a cewar Oyeyemi.

Mai magana da yawun yan sandan ya tuna da wani mashahurin makashi da ya addabi Ijebu-Ode da kewaye da jami'an tsaro suka kashe a irin wannan yanayi farkon watan da ya gabata.

Oyeyemi ta ce Kwamishinan yan sanda, Edward A. Ajogun ya umarci a sanya ido tsawon awa 24 don gano ayyukan bata gari a yankin

A wani labarin daban, tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo ya goyi bayan Muhammadu Buhari a shekarar 2015 duk da cewa ya san 'bai san komai ba' Olagunsoye Oyinlola, tsohon gwamnan jihar Osun ya ce.

Mista Oyinlola ya yi bayanin cewa Mista Obasanjo ya yanke shawarar goyon bayan Mista Buhari ne saboda takaicin gwamnatin Goodluck Jonathan.

Duk da cewa (shi) Obasanjo ya san cewa dan takarar na jam'iyyar All Progressives Congress (APC) ba zai iya tabuka wani abin azo-a-gani ba, amma duk da haka ya goyi bayansa bayan wasu jiga-jigan yan Najeriya sun matsa masa lamba.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel