Jami'an tsaro sun ceto mutane 4, sun damke masu garkuwa 3 a jihar Kaduna

Jami'an tsaro sun ceto mutane 4, sun damke masu garkuwa 3 a jihar Kaduna

- Kwamishanan harkokin tsaron jihar Kaduna ya bayyana yadda aka ceto mutane daga hannun yan bindiga

- Bayan haka an damke mutum uku cikin masu garkuwa da mutanen

Jami'an tsaro sun ceto mutane hudu da aka sace a karamar hukumar Chikun da Kajuru na jihar Kaduna kuma suka damke masu garkuwa uku bayan an kure musu gudu a garin Gajina.

Gwamnatin jihar Kaduna, a jawabin da ta saki ranar Asabar, ta ce jami'an atisayen bugun tsawa sun ceto mata biyu a Gadanan Gwari na karamar hukumar Chikun bayan an sacesu a hanyarsu ta zuwa gona.

Kwamishanan harkokin tsaro da cikin gidan Kaduna, Samuel Aruwan, ya bayyana cewa jami'an yan sandan a farmaki biyu da suka kai, sun kuma ceto mutane biyu da aka sace a Kurmin Idon dake hanyar Kaduna-Kachia a karamar hukumar Kajuru.

Yayin jawabi kan yadda aka ceto matan, Aruwa yace, bisa rahoton sa gwamnatin jihar ta samu, jami'an na sintiri ne lokacin da suka bibiyi yan bindigan kumasuka bude musu wuta, har suka gudu suka bar wadanda suka sace.

Ya ce bayan ceto matan, jami'an sun bi su cikin daji inda sukayi gamo da wasu yan bindigan kuma suka ragargajesu.

Ya kara da cewa daga karshe sun turke yan bindigan a Gajina kuma suka damkesu.

A cewarsa, tuni an mayar da matan wajen iyalansu.

KU KARANTA: Na bar rundunar sojin Najeriya fiye da yadda na tarar da ita, Buratai

Jami'an tsaro sun ceto mutane 4, sun damke masu garkuwa 3 a jihar Kaduna
Jami'an tsaro sun ceto mutane 4, sun damke masu garkuwa 3 a jihar Kaduna
Source: UGC

KU KARANTA: Jerin sunaye: Shugabannin dakarun sojin kasa na Najeriya tun daga 1999 da jihohinsu

A bangare guda, daya daga cikin dalibai matan sakandaren Chibok, Hauwa Halim Maiyanga, ta samu yanci bayan shekaru biyar da yan ta'addan Boko Haram suka kwasheta da kawayenta.

Hauwa na cikin matan makarantan sakandaren gwamnatin mata dake Chibok, jihar Borno, ranar 14 ga Afrilu, 2014.

A cewar TheCable, wata majiya daga gidan Soja ta bayyana cewa hakan ya biyo bayan hare-haren da ake kaiwa inda aka ceto daruruwan mutanen da yan Boko Haram suka sace.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel