Buratai ya mika mulki ga sabon shugaban hafsan sojin kasa, Ibrahim Attahiru (Hotuna)
- Manjo Janar Ibrahim Attahiru yanzu ya zama shugaban hafsoshin sojin kasa
- Attahiru ya karba ragamar mulki daga hannun Janar Tukur Buratai ranar Alhamis
- Ana sa ran sabon shugaban zai jagoranci Sojoji wajen kawo karshen rashin tsaro a Najeriya
Kimanin sa'ao'i 24 bayan sanarwa, an yi taron mika mulki daga hannun wanda ya sauka daga karagar zuwa sabon da shugaban kasa ya nada, a yau Alhamis, 28 ga watan Junairu, 2021.
A wannan taro mai kayatarwa da aka gudanar a farfajiyar taron hedkwatar sojin kasa dake birnin tarayya Abuja, Laftanan Janar Tukur Yusuf Buratai, ya mika tutan fara aiki ga sabon shugaban hafsan Sojin kasa, Manjo Janar Ibrahim Attahiru.
KU DUBA: Mambobin jam'iyyar APC 5,000 sun sauya sheka jam'iyyar PDP
KU KARANTA: Hukumar kula da sadarwa NCC ta fara gudanar da bincike kan saurin karewan 'Data'
Shugaba Muhammadu Buhari ya sallami dukkan hafsoshin tsaron Najeriya a ranar Talata, 26 ga watan Junairu, 2021, kuma ya nada sabbi ba tare da bata lokaci ba.
Mai magana da yawun Buhari, Femi Adesina, ya bayyana haka a shafinsa na Tuwita.
A cewar Adesina, Buhari ya nada Manjo Janar Leo Irabor a matsayin shugaban hafsoshin tsaro; Manjo Janar Ibrahim Attahiru matsayin shugaban Sojin kasa; RA AZ Gambo matsayin shugaban sojin ruwa, da kuma AVM IO Amao matsayin shugaban mayakan sama.
A bangare guda, sakamakon sallaman Laftanan Janar Tukur Buratai matsayin shugaban hafsoshin Sojin Najeriya ranar Talata, ya zama babban hafsa mafi dadewa kan kujerar mulki a tarihin Najeriya.
Daily Trust ta bayyana cewa Janar Buratai dan asalin jihar Borno ya yi watanni 66 matsayin shugaban Sojojin kasan Najeriya.
Daga Buratai sai marigayi Janar Sani Abacha wanda yayi watanni 60 kan kujerar
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng